Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kotun Amurka ta yanke wa Sarkin gargajiya daga Jihar Osun, Oba Joseph Oloyede, wanda ake kira Apetu na Ipetumodu, hukunci bayan kama shi da laifin karkatar da kuɗaɗen tallafin annobar cutar Korona.
Hukuncin ya biyo bayan shigar da ƙarar da ofishin babban lauyan gwamnatin Amurka a Jihar Ohio ya yi, inda aka tabbatar da cewa, ya jagoranci aikace-aikacen bogi, domin karɓar tallafin da Gwamnatin Amurka ta ware, amma tallafin da ya karɓa ya karkatar ne ga ‘yan kasuwa da ƙungiyoyi a lokacin ɓarkewar annobar cutar ta Korona.
Rahoton ofishin lauyan Amurka ya ce tsakanin Afrilun 2020 zuwa Fabrairun 2022, Sarkin da abokinsa Edward Oluwasanmi suka tura buƙatun bogi don samun rancen tallafin Korona.
An gano cewa Oloyede ya mallaki kamfanoni guda biyar da wata ƙungiya, sannan ya yi amfani da su wajen tura bayanan ƙarya.
A gefe guda, abokinsa Oluwasanmi ya mallaki kamfanoni guda uku da aka yi amfani da su wajen karɓar kuɗin.
Daga cikin abin da suka karɓa, kusan Dala miliyan 1.7 aka samu ta hannun Oloyede, yayin da Oluwasanmi ya samu Dala miliyan 1.2, wanda gaba ɗaya ya kai Dala miliyan 4.2 (Biliyan N6.4).
Bincike ya nuna cewa Oloyede ya yi amfani da wasu daga cikin kuɗin wajen sayen fili, gina gida da kuma mallakar wata mota mai tsada.
Haka kuma, ya yi amfani da sunayen wasu abokan cinikinsa wajen neman rance, inda shi kuma ya riƙa karɓar kaso tsakanin kashi 15 zuwa 20 daga abin da suka samu.
Bayan karɓar kuɗin, bai bayyana su ba ga hukumar haraji ta Amurka (IRS) ba, lamarin da ya kara tsananta masa tuhumar zamba da karya a haraji.
Kotun ta tabbatar da cewa Oloyede ya jagoranci aikace-aikacen bogi har guda 38, wanda hakan ya sa aka amince da rancen da ya kai jimillar Dala miliyan 4.2.
Abokin haɗin gwiwarsa, Edward Oluwasanmi, wanda shi ma ke da shekaru 62 daga garin Willoughby, an yanke masa hukuncin shekara biyu da watanni bakwai a kurkuku a watan Yuli.
An kuma umarce shi ya dawo da fiye da dala miliyan 1.2 da kuma miƙa kadarorin da ya mallaka daga kuɗin damfara.
Baya masa daurin sama da shekara hudu, kotun ta umarci Sarkin ya biya fiye da Dala miliyan 4.4, sannan ya sallama gidansa da sauran kadarorin da ya samu daga haramtacciyar hanya.
Hukumomin FBI, IRS da ofishin binciken sufuri ne suka jagoranci binciken tare da kwamitin yaƙi da damfarar tallafin annobar Korona.
