Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kungiyoyin fararen hula a Nijeriya sun nemi a gaggauta sakin shugaban Falasɗinawa Ramzy Abu Ibrahim da mambobinsa ba tare da gindaya wani sharaɗi ba.
Sun yi gargaɗin cewa kama su da aka yi ya saɓa wa tanadin kare haƙƙin ɗan’adam kuma ka iya jefa Nijeriya cikin rikicin Gabas ta tsakiya.
Wannan saƙo na cikin wata sanarwa ta haɗin guiwa da Omotaje Olawale Saint na ƙungiyar WorkBond International Network (WIN) da Kunle Ajayi na ƙungiyar Wizeman of United Action for Democracy (UAD), suka sa wa hannu tare da amincewar sauran ƙungiyoyi da dama, inda suka bayyana kama Abu Ibrahim da cewa yana da alaƙa da fafutukar da yake yi ta harin Isra’ila a Gaza.
Gamayyar ƙungiyoyin sun ce kama jagoran Falasɗinawa na zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriya ta ƙulla yarjejeniya kan tsaro da musayar bayanan sirri da ƙasar Isra’ila.
Lamarin da ta bayyana da “abin damuwa”.
Sannan ya sun buƙaci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya kaucewa zama karen farautar Isra’ila, tana mai bayyana cewa tilas ne Nijeriya ta cigaba da riƙo da tanadin kundin tsarin Nijeriya.
“Nijeriya tana ƙoƙarin wasa da wuta,” ƙungiyar ta faɗa, tana mai cewa, “Bai kamata Nijeriya ta bari a ja ta cikin rikicin yankin Gabas ta tsakiya ba.
“Ya kamata mu san Nijeriya na fama da kanta ne ta fuskar tattalin arziki da matsalar tsaro da rikicin manoma da makiyaya sauran munanan abubuwa. Bai kamata Nijeriya ta rufe ido ta ba wajen zama makami a faɗan da ake yi tsakanin Falasɗinawa da Isara’ila.”
Abu Ibrahim na kan gaba wajen yin magana game da hare-haren da ake kai wa fararen hula a Gazafs kashe ‘yan jaridu.
“Ba tare da ƙumbiya-ƙumbiya ba, duk wani mai sanin ya kamata ba zai lamunci zama karen farauta a yankin da ake a yankin Gabas ta tsakiya,” a cewar sanarwar.
Wannan mataki a cewar ƙungiyoyin, mataki ne na mara wa Falasɗinawa baya waɗanda suke cikin uƙuba na tsawon lokaci.
ƙungiyar ta kuma ce mara wa Falasɗinawa baya ba laifi ba ne, haka ma fafutukar faɗar albarkacin baki.
Sun ce bai kamata Nijeriya ta zama makamin rufe bakin masu bayyana ra’ayi ba ko kare muradan ƙasshen waje.
“Kama Abu Ibrahim da ‘yan ƙabilarsa kai tsaye take ‘yancin albarkacin baki ne da take ‘yancin ɗan’adam.”
Kuma sun ce kama shi ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Nijeriya da dokokin duniya wanda Nijeriya ta aminta da su.
“Muna kira da a kafa ƙasshen biyu masu cin gashin kansu a yankin Gabas ta tsakiya domin kawo na ƙarshen dambarwar da ake yi,” ta faɗa.
ƙungiyar ta ce wannan ce hanya ta samar da adalci da zaman lafiya.
Sun kuma buƙaci gwamnatin Nijeriya da ta mutunta ‘yancin Falasɗinawa da tabbatar da cewa ba sa fuskantar kowacce iriyar cuzgunawa.
Sannan sun buƙaci gwamnatin Tinubu da ta sake duba yarjejeniyar da ta ƙulla da ƙasar Isra’ila wanda ka iya tauye ‘yancinta.
