Gwamnatin Kano ta bada fili don gina rukunin gidaje a Bichi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da wani katafaren filinta da ke Ƙaramar Hukumar Bichi don gina rukunin gidaje mai guda 2000 wanda Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Bichi, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar Bichi zai yi a cikin garin Bichi.

Shugaban Majalisar karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ya bayyana haka a taron gangamin wayar da kan al’umma da Jami’ an Ma’aikatar Raya Karkara da Cigaban Al’umma ta jiha ke gudanarwa a yankunan kananan hukumomin jihar nan, domin sanin abin da jama’a suke bukata da kuma abubuwan dake damunsu, wanda aka yi a sakatariyar Karamar Hukumar Bichi.

Mai Fata ya ce, bayar da filin don gina gidajen, abu ne da zai taimaka wajen cigaban karamar hukumar da kuma kara bunkasa harkokin tsaro da tattalin arzikin al’ummar yankin da jiha baki daya.

Ya kuma ce filin da za a yi gidajen, Fulani ne Makiyaya da aka tasa aka kuma samar da gurin da aka tsugunar da su domin cigaba da harkokin su na kiwo.

A bangaren ta, mai taimaka wa Gwamna kan harkokin Fulani Makiyaya, Hajiya Rukayya Umar Gadon Kaya, wadda tana daga cikin wakilan da suka ziyarci karamar hukumar, ta sake gabatar da bukatar da Fulani ke da ita ga shugaban karamar hukumar na rashin ruwan sha da guraren kiwo da matsalar tsaro da kashe shanunsu da ake kadewa akan tituna, musamman Fulanin dake zaune a rugar bayan asibitin Bichi domin a taimake su a dauki matakin magance matsalolin, inda kuma nan take shugaban Majalisar karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ya tabbatar da cewar tuni Gwamnati ta dauki mataki akan al amarin da ya shafi samar da cigaban Fulanin a sabon gurin da aka mayar da su kamar yadda jami’ar hulɗa da jama’a ta ƙaramar hukumar Jamila Abdullahi R/Lemo ta bayyana.

“Inda aka gina musu suka koma, da za ki je a yanzu, tuni aka yi musu rijiya mai sola wadda ba ma sai sun buga da hannu ba, sola ce take zuko musu ta tara musu a tanki su tsiyaya kawai su sha. Sannan mai girma Dan Majalisa ya ba su kudi naira dubu dari bibiyu (200,000.), ya kuma ce duk wanda ya cire rumfarsa ya je can ya yi daben siminti a wajen.” In ji shi.

A lokacin taron wasu daga cikin kungiyoyin al’umma daga sassan karamar hukumar da suka halarta, sun gabatar da wasu bukatun su da suke son Gwamnati ta kawo musu
dauki.

1- “Makarantarmu ta matan aure ta Dangawo, muna da matsalar bilok. A kalla mun yi kusan shekara goma muna karatu a wajen, amma yanzu haka makarantar ta lalace sakamakon dama gida ne aka ba mu muke karatu a ciki.” In ji wakiliyar makarantar matan aure ta Dangawo dake Bichi.

2- “Muna son gwamnati ta taimaka mana da wuraren da za mu dinga noma Wanda za a ce namu me ba na wani ba, ko kuma wata gwamnatin ta zo ta fisge ta ba wasu. Muna so a taimaka mana da mata da matasa saboda muna so mu yi noman, amma ba mu da wurin noma.” In ji Rakiya Abdullahi Muhd daya daga cikin wasu kungiyoyi masu kananan sana’o’i a Karamar Hukumar Bichi.

3- “Muna kai koke ga mai girma Gwamna tun daga matakin karamar hukuma, a kan assasa yi mana makarantu a rugagemu na Fulani, domin samun yin ilimin fasaha da koyarwa da gogewa da wayewar kan dan’adam.” In ji Aminu Rabi’u mataimakin shugaban Kungiyar Miyatti Allah dake Karamar Hukumar Bichi.

An dai kammala taron da addu’ oi na musamman domin dorewar albarkar daminar bana da bunkasar zaman lafiya da tattalin arzikin yankin da jihar Kano da ma kasa baki daya.

By Babaji