Ɗalibai 996 za su zauna jarrabawar samun gurbi a makarantun Katsina na musamman

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ɗalibai 996 Cikin 2,172 daga mazaɓu 361 na Jihar Katsina da za su zauna jarrabawar tantancewa da za su sa mu gurbin karatu a makarantu na musamman na gwamnatin Jihar Katsina.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanar da haka a bayan kammala taro da shugabannin ƙananan hukumomi 34 a gidan gwamnatin jihar.

Ya bayyana yadda za’a gudanar da tantancewa da kuma ɗaukar ɗaliban da za’a ɗauka a makarantu uku na musamman (Special Schools) da gwamnan zai ƙaddamar a garin Raɗɗa, Dumurƙul, da Jiƙamshi.

Taron wanda ya ƙunshi Shugabannin ƙananan hukumomi 34, sakatarorin ilimi na ƙananan hukumomi, tare kuma da jami’an ilimi na kwamitin cikin gaban al’umma na mazaɓu 361 (Community Learning Officers) na shirin CDP.

Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana yadda gwamnatin shi ta ɗauki nauyin karatun ɗalibai ƴan asalin jihar bisa cancanta domin su karanci likitanci a ƙasar Masar, da kuma ilimin zamani na Artificial Intelligence da Biotechnology a ƙasar Sin, wanda ya ce ya kammala biyan duk wani kuɗin karatun su na tsawon shekarun da zasuyi har su dawo gida.

Haka kuma ya ce ɗaya daga cikin abubuwan da yayi alƙawari a fannin ilimi shine samar da makarantu na musamman ga ƴaƴan talakawa da Allah yaba basira “Gifted” domin samun damar yin ingantaccen ilimi domin al’umma ta amfana da basirar su.

Ya cigaba da cewa tun da ƴaƴan masu hali suna zuwa makarantun kuɗi domin samun ingantaccen ilimi, “ya kamata suma ƴaƴan talakkawa su samu irin wannan damar, domin suma su samu damar zama wani abu a duniya kuma watarana su gina Jihar Katsina.

Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa za’a bayar da guraben karatun ne bisa cancanta, kuma kowace mazaɓa cikin mazaɓu 361 za ta samu wakilci.

Tsarin jarrabawar tantancewar zai kasance kowace mazaɓa za ta bayar da ɗaliban da suka fi ƙoƙari guda shida, biyu daga Aji 6 na firamare zuwa JSS1, biyu daga JSS1 zuwa JSS2, sai kuma biyu daga JSS2 zuwa JSS3.

Dukkanin ɗaliban da za’a ɗauka a wannan makarantu, gwamnatin Katsina ce za ta ɗauki nauyin karatun su,da samar masu da na’ura mai kwakwalwa da ma damar amfani da yanar gizo, tare da ingantattun malamai da kuma sauran abun buƙata.

Gwamna Raɗɗa ya kuma jaddada cewa ɗaliban da suka fito daga gidajen talakawa ne kawai za su amfana da makarantun saboda duk wanda yake da kuɗi zai iya kai yaran shi makarantar kuɗi.

Gwamnan yace za’a kammala makarantar ta garin Raɗɗa a cikin wannan watan, ta Dumurƙul da Jiƙamshi sai cikin ƙarshen shekarar nan, amma duka ɗalibai 996 da za’a ɗauka lokacin a za su fara karatu a ta garin Raɗɗa, kuma za’a cigaba da ɗaukar ɗaliban duk shekara.

“A shiri na na aiwatar da wannan makarantu ina ganin Jihar Katsina ta gobe ne ba wai yau ba, kuma buɗe wannan makarantu ba wai yana nufin sauran makarantun gwamnati za su daina samun kulawa ba,”inji Dikko Raɗɗa.

Za’a gudanar da wannan jarabawar tantancewar a cibiyoyi bakwai, wanda suka haɗa da Katsina College Katsina, GGSS Funtua, GDSS Daura, GPSS Dutsin-ma, GUSS Malumfashi, GDSS Kankia, sai GDSS Mani.

Gwamnan Raɗɗa ya umarci shugabannin ƙananan hukumomi da su ɗauki nauyin kai wa da ɗauko ɗaliban ƙananan hukumomin su zuwa wajen wannan jarabawa.

Ya kuma roƙi shugabannin da za su kula da wannan tantancewa suyi gaskiya ba tare da nuna banbanci ba, ya bayyana ma su wanda yaci amana Allah ba zai bar shi ba.

By ukarofi