
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Dokoki ta Jihar Kebbi tabbatar da dokar yin gwajin lafiya ga masu shirin aure a tsakaninsu a jihar.
Ƙudirin, wanda kwamitin lafiya na majalisar ya ɗauki nauyinsa, ya tsallake karatu na ɗaya, biyu da na uku kafin Kakakin majalisar, Muhammad Usman ya tabbatar a ranar Alhamis yayin zaman da suka saba yi a zauren majalisar.
Daga cikin ababen da dokar ta ƙunsa akwai tabbatar da yi gwajin ajin jini (genotype) da dangin jini (blood group) a asibitocin da aka amince da su.
Wajibi ne kuma a yi gwajin a watanni uku ko sama da haka kafin aure, sannan a maimaita a sati biyu kafin ranar aure, yayin da za a karɓi shaida daga ƙwararrun likitoci kaɗai.
A yayin da gwamnan jihar ya sanya hannu akan dokar, za riƙa umartar masu niyyar yin aure su gabatar da rahoton gwajin lafiya kafin a ɗaura musu aure.
Haka kuma ƙudirin ya ƙunshi hukunta duk limami ko sarkin ko wani da ya ɗaura aure ba tare da tabbatar da shaidar rahoton gwajin lafiya ba ta hanyar cin sa tarar N200,000 ko kuma wata shida a gidan kaso.
Sannan, duk likitan da ya bada rahoton ƙarya, za a ci shi tarar miliyan N1 ko shekara guda a kurkuku.
