Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Hukumar tsaro ta Civil Defence (NSCDC) a Jihar Gombe ta kama mutane huɗu a lokuta daban-daban bisa zargin lalata kayayyakin wutar lantarki da kuma fyaɗe kan yarinya ƙaramar ƴar shekara 13.
Da yake gabatar da waɗanda ake zargi a hedikwatar hukumar, Kwamandan jihar, Idris Jibrin, wanda jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SC Buhari Sa’ad ya wakilta, ya ce an cafke wasu maza biyu bisa zargin lalata muhimman kayayyakin gwamnati.
Ya bayyana sunayensu da Salisu Mohammed, mai shekara 18, daga unguwar Idi Gombe, da kuma Mohammed Dahiru Babayo daga Unguwar Dawaki.
Sa’ad ya ce an gano wayoyi na aluminium da aka lalata a shagon Salisu dake Unguwa Uku.
Ya ƙara da cewa bincike yana gudana kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala binciken.
A wani lamari daban, hukumar ta kuma cafke wani mutum mai shekara 48, Ibrahim Haruna, wanda yake sana’ar ɗinki tare da ɗansa Abdullahi Ibrahim mai shekara 15, bisa zargin yiwa yarinya ƙarama ƴar shekara 13 fyade a lokuta daban-daban.
A cewar Sa’ad, Haruna ya yi wa yarinyar fyaɗe ne a shagonsa, yayin da ɗansa Abdullahi ya aikata hakan a gidansu dake unguwar Jekadafari a ƙaramar hukumar Gombe.
Ya ce bincike kan lamarin ya kammala, kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a kotu.
Sai dai Haruna ya musanta zargin, inda ya ce ya taɓa yarinyar ne kawai cikin wasa amma bai yi lalata da ita ba.
Hukumar NSCDC ta ce ba za ta bayyana sunan yarinyar ba domin kare mutuncinta bisa ƙa’idar kare haƙƙin yara.

