
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimanin mutane 29 ne suka rasu yayin da aka ceto wasu guda 50 a lokacin da wani kwale-kwale da ya yi jigilar fasinjoji ya kife a wani kogin Jihar Neja.
Al’amarin ya faru ne a ranar Talata a wani ƙauye mai suna Gausawa da ke yankin Malale a Ƙaramar Hukumar Borgu.
Darakta-Janar na Hukumar Bada Agajin Gaggawa a jihar (NSEMA), Alhaji Abdullahi Baba Arah ya tabbatar aukuwar lamarin a Minna, ranar Laraba.
Ya ce, kwale-kwalen ya taso ne daga Ƙauyen Tungan Sule a yankin Shagunu inda ya ɗebo mutane guda 90 da suka haɗa da mata da yara da nufin zuwa Dugga ta’aziyya.
Ya bayyana cewa, hatsarin ya faru ne sakamakon ɗaukar mutane sama da kima da kuma karo da wani kututturen bishiya.
Shugaban na NSEMA, ya ƙara da cewa, an samo gawawwaki guda 29 da ceto mutane 50 yayin da 2 kuma suka yi ɓatan dabo.
Ana cigaba cigaba da bincike domin gano waɗanda suka ɓacen, kamar yadda ya faɗa.



