
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar kula da Gidajen Gyaran Hali NCoS, ta fitar da bayanan fursunonin da suka tsere daga gidajen yari biyu, wato na Keffi a jihar Nasarawa da Ilesa a jihar Osun yayin da lamuran fashin magarƙama ya fara yawaita a Nijeriya.
NCoS ta fitar da bayanan fursunonin ne, waɗanda galibinsu munanan laifuka suka aikata da suka haɗa da fashi da mallakar makamai ba bisa doka ba.
A safiyar Talata, 12 ga watan Agusta, fursunoni 16 suka tsere daga kurkukun Keffi da ke Nasarawa bayan sun banƙara jami’an tsaron gidan.
A cewar sanarwar da Kakakin NCoS, Umar Abubakar, ya fitar, fursunonin sun yi wa jami’an da ke bakin aiki dirar mikiya, inda suka yi galaba a kansu sannan suka tsere.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an sake kama fursunoni bakwai daga cikin waɗanda suka gudu, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike da neman sauran tara da suka rage.
Kurkukun Keffi ya fitar da sunayen waɗanda suka tsere kamar haka:
Mohammed Mohammed (24), Kaduna
Yusuf Hassan (21), Adamawa
Shehu Abubakar (20), Kaduna
Abubakar Jibrin (18), Plateau
Abubakar Musa (30), Kaduna
Bilyaminu Usman (20), Bauchi
Yusuf Abubakar (18), Jigawa
Adamu Anas (19), Gombe
Danlami Baka (27), Bauchi
Haka ma na Ilesha, fursunonin da suka tsere sune: Eze Nweze, Tobi Akin, Matthew Ogunjimi, John Michael, Ninalowo Yusuf da Olalekan Ajofoyinbo.
Tuni NCoS ta sanar da cewa za a biya ladar Naira miliyan 5 ga wanda ya taimaka da bayanai aka kama sauran waɗanda suka tsere.
