Gidauniyar Zakka da ke Legas ta bayar da rancen N1m ga wasu ƙananan ’yan kasuwar Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gidauniyar Zakka da Sadaƙa da ke Legas ta raba rancen Naira miliyan ɗaya ga wasu ƙananan ‘yan kasuwar Zamfara guda biyu, Malama Habiba Abdulsam da Malam Abba Bello, da nufin taimaka musu wajen bunƙasa ƙananan sana’o’insu.

Da yake gabatar da cekin kuɗin ga waɗanda suka ci gajiyar tallafin a Gusau yau Lahadi, babban darakta na gidauniyar Sulaiman Olagunju ya bayyana cewa gidauniyar ta zaɓo waɗanda suka ci gajiyar shirin ne domin taimaka musu wajen bunƙasa ƙananan sana’o’insu.

Ya ce za su biya bashin ne ba tare da sanya kuɗin ruwa ba ga waɗanda suka ci gajiyar ba, inda ya ce an bai wa kowane mai cin gajiyar kuɗi Naira 500,000, wanda zai biya a cikin shekara guda.

Ya kuma bayyana cewa gidauniyar ta ware Naira 500,000, domin biyan kuɗin makaranta ga ɗalibai marasa galihu da suka fito daga makarantun firamare, ƙanana da manyan sakandire a jihar ta Zamfara.

A cewar sa, wannan karimcin na da manufar rage wahalhalun zamantakewar al’umma a tsakanin mutane masu rauni da kuma ba su damar zama masu dogaro da kai.

Babban daraktan gidauniyar Olagunju wanda ya samu wakilcin kodinetan gidauniyar na Jihar Zamfara a wajen gabatar da cekin kuɗin, Sulaiman Ibrahim Tudu, ya bayyana cewa gidauniyar ta zaɓo marayu 13 da za su samu damar shiga jami’a bayan kammala karatunsu na sakandare ta hanyar shirin gidauniyar a bana.

Ya kuma bayyana cewa shirin ya shafi jihohi 19 na Arewa ciki har da jihohin Kudu, inda ya ce an zaɓo makarantu bakwai a Zamfara don bai wa ɗaliban tallafin karatu.

Ya bayyana cewa gidauniyar ta ɗauki nauyin duk kuɗin makaranta ga ɗaliban da aka zaɓo domin kammala karatunsu na ƙanana da manyan sakandare a ƙarƙashin shirin.

By ukarofi