Badaƙalar matata: Tsohon Shugaban NNPC, Mele Kyari ya miƙa kansa ga EFCC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Laraba Tsohon shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL, Mele Kyari ya kai kansa ga Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) domin gudanar da bincike akansa.

Rahotanni sun bayyana cewa, Kyari ya isa hedikwatar hukumar ne a Abuja da misalin ƙarfe 2:15 na rana bayan EFCC’n ta gayyace shi da nufin yi masa wasu tambayoyi akan wasu al’amura da suka shafi zamansa a muƙamin shugaban kamfanin.

Majiyoyi daga hukumar sun tabbatar da cewa zuwan Kyari ofishin bai rasa nasaba da bincike akan Dala biliyan 7.2 da aka ware na gyare-gyaren matatun gwamnati da kula da su, wanda a tsawon lokaci aka sanya su a sahun kuɗaɗen da ake zargin sauya akalarsu aka yi.

A kwana nan ne EFCC ta sanya Kyari a sahun waɗanda ta ke sanya wa harkokinsu ido.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci a rufe asusun bankuna guda huɗu da aka alaƙanta su da shi bisa binciken badaƙalar kuɗaɗe.

By Babaji