
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Matatar Ɗangote ta sake rage farashin litar fetur zuwa N820 yayin da take shirin fara dakon sa kai-tsaye ga gidajen mai a ranar Litinin, 15 ga watan Satumba, 2025.
Ta sanar da haka ne ta kafar X a ranar Alhamis, inda ta ce asalin farashin daga wajenta shine N820 ga kowace lita yayin da za a samu banbancin farashi a famfuna bisa la’akari da waje.
Za a riƙa sayerwa a jihohin Legas, Ogun, Oyo, Ondo, Osun, da Ekiti akan N841 yayin da a Abuja, Delta, Ribas, Edo, da Kwara kuma za a ke saya a N851.
Hakan na nufin matatar za ta riƙa kai wa kwastomominta a Legas da jihohin kudu maso yamma akan ragin N19 yayin da Abuja da sauran jihohin Arewa ta Tsakiya da na Kudu maso Kudu su kuma a ragin N34.

Matatar ta bayyana cewa dakon mai a kyauta ga gidajen man kwastomominta a faɗin sassan ƙasar, ƙarin alfanu ne a gare su a ƙarƙashin shirin nata.
