Ba za mu iya daƙile manyan laifukan zamani da makaman da ba, inji Sufeto Janar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sufeto-Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya bayyana cewa masu aikata miyagun laifuka a yanzu suna amfani ne da makamai masu ƙarfi sama da na hukumomin tsaron ƙasar.

Saboda haka ya ce, sai an samar wa jami’an tsaro makamai na zamani kafin su iya daƙile ayyukan ɓata-gari a sassan ƙasar.

Da yake jawabi game da ƙalubalen tsaro da Nijeriya ke fuskanta, Shugaban ƴan sandan ya bayyana cewa ƙungiyoyin masu aikata manyan laifuka suna da kimtsi da ɗaukar nauyi yadda ya dace da su da kuma alaƙar aiki a mataki na ƙasa-da-ƙasa.

Ya bayyana cewa, ƙalubalen da suke fuskanta a kullum yana sauyawa duba da yadda ƙungiyoyin ta’addanci ka ƙara ƙarfi.

Sufeton ya kuma ce, ba zai yiwu jami’ansu su yaƙi ta’addanci da kayan aikin a da ake amfani da su a ƙarni na 20 a wannan lokaci na ƙarni na 21 ba bisa la’akari da ƙarfin kayan aikin miyagu.

A saboda haka ne suke amfani da fasahar zamani wajen hasko wuraren da ake aikata laifuka, waɗanda a cewarsa ba da su ke yaƙar miyagun ba, sai dai ababe ne na lalura da ke taimaka wa atisaye.

By Babaji