Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Ranar 14 ga Augusta,2025, da magariba, wasu yan bindiga da aka ƙiyasta sama da 60 ɗauke da muggan makamai sun far wa garin Dayi inda su ka wuce kai tsaye zuwa gidan Hon. Nasiru Dayi da ke tsakiyar garin kuma su ka kama shi su ka tafi da shi, shi kaɗai, duk da ƙoƙarin tirjiya da ya yi musu, kuma ance sun ja shi a ƙasa yadda su ka yi masa raunuka a kafaɗunsa da bayansa.
Bai fi yan kwanaki ba mun yi waya da shi ya ke ce min zai shigo Kano zai ga CMD na Dala Orthopedic Hospital wanda abokinsa ne. Akasari idan ya zo Kano ya kan sauka a gida na har ya gama harkokinsa. Ya ce min an gayyace shi cikin wani kwamiti na dattawan APC a Malumfashi domin tsara yaƙin neman tazarcen Gwamna Dikko Raɗɗa, kuma za su zauna a Katsina da Gwamna. To amma sakamakon haɗarin da Gwamnan yayi, an dage zaman sai ya dawo daga asibiti. To a wannan tsakani ne waɗancan ƴan bindiga suka shiga Dayi su ka ɗauke shi. Kuma da alamu dai cune ne na informants kamar yadda ya ke faruwa a Jihar Katsina.
Na sami tashin hankali sosai bayan na yi magana da iyalinsa inda ɗan sa Aminu ya shaida min cewa masu garkuwan sun kira sun nemi Miliyan 20. Na san cewa Malam Nasiru ba shi da waɗannan kuɗaɗe a halin yanzu, kuma su kansu waɗanda su ka cuna shi na tabbatar su na sane da cewa ba shi da komai a yanzu. Hatta noman da ya saba yi a duk shekara sama da shekaru talatin, a bana da bakinsa ya shaida min cewa noman ba zai yiwu ba. Kuma ko gidansa aka saka a kasuwa ba zai kawo wannan kuɗi ba.
Mun yi shawara a tuntuɓi abokan hulɗarsa domin tsohon ɗan siyasa ne wanda ya yi kansila har zuwa matakin mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Malumfashi. Kuma ɗan boko ne ya san mutane. A jerin farko mutanen da aka fara tuntuɓa, wanda shi da kansa Alhaji Nasirun ya ce a tuntuɓa, sun haɗa da maigidansa Halilu Ahmed Getso, fitaccen ɗan jaridar kuma elder, da zummar ya tuntuɓar masa Hon Barau Jibrin ya kawo masa ɗauki. Sannan na turawa Balarabe Ilela, tsohon Darakta Janar na NBC lokacin Buhari wanda na san cewa mutuminsa ne sosai da sosai domin shi Alhaji Nasiru ya taka rawa sosai wajen nemawa Alhaji Balaraben waccan kujera da ya bari. Haka nan Alhaji Nasiru ya nemi ɗansa da ya tuntuɓi tsohon kakakin soji, Rtd General Kuka Sheka, wanda abokinsa ne kuma sun yi makaranta tare a Kafancan inda su ke da ƙungiyar old boys.
Bayan kwashe kwanaki a hannun yan ta’adda, sun kira Aminu da barazanar sun ji shiru kuma Alhaji Nasiru na cikin mawuyacin halin rashin lafiya sakamakon raunukan da ya samu, idan ba’a kawo kuɗi ba, sun bada wasu kwanaki, cewa za su mayar da fansar miliyan talatin ko su kashe shi.
Wannan Abu ya daɗa tayar mana da hankali, don haka sai na tuntubi abokin aiki Maiwada Dan Malam, na yi masa bayanin halin da ake ciki ko zai taimaka ya yiwa Gwamna Dikko Raɗɗa magana. Duk da dai na san cewa a zahiri gwamnatoci na nesanta kansu daga bada kuɗin fansa a hukumance, amma dai sanin cewa shi Gwamna Dikko ya san Alhaji Nasiru tun kafin ya zama Gwamna, domin a lokacin ya na SMEDAN mun je Abuja tare da Alhaji Nasiru ya je ofishinsa nema min wata alfarma.
Daga baya, shi Halilu Ahmed Getso ya aiko yayansa da kuɗi 100,000 a kawowa iyalin Alhaji Nasiru su yi cefane kuma ya ce bai iya samun magana da Hon Barau Jibrin ba. Shi kuma Gen. Kuka Sheka ya tattara a group ɗinsu an tara 700,000. Haka zalika shi Balarabe Ilela da Aminu ya sake tuntuɓarsa ya ce Idan kidnappers din sun sake kira ace akwai miliyan biyu, wadda shi ya ɗauki alƙawarin zai bayar.
Bayan masu garkuwan sun kira an ce akwai miliyan biyu, Aminu ya sha zagi ta uwa ta uba, kuma sun ce ba sa ma son ko kwabo tunda an raina musu hankali don haka za su kashe shi kawai, kuma su ka kashe waya.
Wannan audio nasu ya sake tada hankula inda na nemi lambar Gwamna Dikko Radda kai tsaye daga wasu makusantansa sosai, kuma na tura masa da voice note na appeal inda na nemi Gwamna a matsayinsa na mutumin Hon Nasiru Dayi, kuma wanda yake cikin kwamitin siyasa na APC a Malumfashi domin tazarcen Gwamna, amma ba a official capacity ba, da ya ceto ran wannan mutum. Na haɗa masa da lambar Aminu domin ya tuntubi iyalin kai tsaye. Bayan kwanaki ban sami wani bayani ba kuma Aminu ya ce ba wanda ya kira shi, na sake tuntubar Maiwada Dan Malam, wanda bayan tabbatar min da cewa haƙiƙa lambar da aka bani ita ce wadda Gwamna Dikko ke amfani da ita, ya ce lallai zai ga saƙon kuma inshallah zai yi responding domin ya na ta ƙoƙarin yadda za’a yi sulhu da ƴan ta’addan a faɗin jihar, sannan lamarin Nasiru Dayin babba ne.
To har a jiya dai bayan tuntuɓar Aminu, na sami bayanin cewa a yanzu dai kuɗin da ke hannunsu miliyan 2.7 ne, amma Balarabe Ilela bai turo da nasa ba tukuna, kuma kwamitin dattawan Malumfashi a taron su, shugaban ma’aikatan Gwamna ya bayar da 300,000. Wato a ƙasa kenan idan an yi jumla, har da wannan 300,000 da miliyan biyu da Balarabe Ilela ya alƙawarta, kuɗaɗen za su zama miliyan 5 kenan.
Ina son in yi amfani da wannan dama na yi kira ga Hon Barau Jibrin da Gwamna Dikko Raɗɗa, su dubi girman Allah su ceto rayuwar wannan ɗan tahaliki, duk wanda ya sanshi ya san cewa mutum ne karimi wanda ya rayu ya na bautawa jama’ar ƙaramar hukumar sa ta Malumfashi da Katsina, kuma gudunmuwarsa ba ta ƙare ba. Allah ya basu Ikon taimakawa kuma Allah ya kawo mana ƙarshen wannan masifa.
A ƙarshe kuma mu sani cewa wannan masifa ba Allah ne ya ɗora mana ba, al’ummar Arewa ita ta ƙirƙirawa kanta wannan yanayi saboda watsi da muka yi da kula da juna da barin talauci ya mamaye ko’ina tare da rashin dabbaka adalci musamman daga waɗanda aka baiwa amanar dukiyar al’umma. Ko dai mu gyara, ta hanyar rarraba arzikin kasa da samarwa matasa aiki, ko kuma masifu salo-salo su ci gaba da sauka a yankin. Allah ya iya mana.
