Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Aƙalla yara 10 ne suka rasa rayukansu a Jihar Neja sakamakon ɓullar cutar mashaƙo a ƙananan hukumomin Agaie da Bida.
Rahotanni sun ce an kai yaran da suka rasu zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya (FMC) da ke Bida, inda suka gamu da matsala sakamakon kamuwa da cutar duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi.
Majiyoyin cikin gida sun bayyana cewa an kuma sami ƙarin asarar rayuka a yankunan karkara a faɗin ƙananan hukumomin biyu tun bayan ɓarkewar cutar, kodayake har yanzu ba a tabbatar da ainihin alƙaluman ba.
Wannan lamari ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin, waɗanda ke yin kira da a gaggauta ɗaukar matakin hana yaɗuwar cutar.
Wani mazaunin Bida, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya koka da yadda adadin wadanda suka mutu ya ƙaru, ya kuma yi kira da a kawo musu ɗaukin gaggawa da magunguna.
“Wannan al’amari ne na rayuwa da mutuwa, kuma muna kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta samar da magunguna ga manyan asibitocin Bida da Agaie domin daƙile yaɗuwar cutar zuwa wasu yankuna,” inji mazaunin garin.
Da yake tabbatar da ɓullar cutar, babban sakataren ma’aikatar lafiya ta manyan makarantu, Mohammed Gana, ya ce gwamnati tare da haɗin gwiwar abokan hulɗar lafiya sun ɗauki matakan ɗaukar matakan gaggawa. A cewarsa, ana ɗaukar matakan samar da magunguna, da karfafa sa ido, da daƙile yaɗuwar cutar.
Mashaƙo cuta ce mai saurin yaɗuwa wacce ta fi shafar maƙogwaro da hanyoyin iska, tana samar da gubar da ke lalata zuciya da ƙoda
Yana iya zuwa da mutuwa idan ba a kula da shi ba, musamman a tsakanin yara.
Hukumomi sun ce allurar rigakafi na yau da kullum shi ne matakin kariya mafi inganci.
Don haka ma’aikatar lafiya ta jihar Neja ta buƙaci iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun samu cikakkiyar alluran rigakafin cutar tare da shawartar jama’a da su kai rahoto ga cibiyoyin lafiya mafi kusa.
