Ƙungiyar Dattawan Arewa ta buƙaci gwamnonin arewa maso yamma su rungumi yin sulhu da ‘yan bindiga

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya ta yi kira ga gwamnonin Arewa maso yamma da su haɗa kai da ƙungiyar mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro da sauran jami’an tsaro wajen rungumar tattaunawa da ‘yan bindiga a matsayin hanyar kawo ƙarshen tashe-tashen hankula.

A yayin da yake magana a Kaduna a ranar Talata, ko’odinetan ƙungiyar, Yusuf Abubakar, ya ce, ƙungiyar ga gamsu da ƙoƙarin da ofishin NSA, Malam Nuhu Ribadu, ke yi da sauran masu ruwa da tsaki wajen amfani da hanyar lumana wajen dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso yamma.

“Muna murna da matakan da ake ɗauka. Bayan tafiya da na yi daga Sakkwato zuwa Gusau da Funtua zuwa Zariya, na lura an samu zaman lafiya.”

“Idan aka kwatanta da baya, tsaro ya inganta, masu tafiy-tafiya yanzu hankalinsu a kwance,” ya faɗa.

Abubakar ya buƙaci gwamnoni da su rungumi hanyar tattaunawa a maimakon zuwa gaisuwar ta’aziyya da kuma ayyukan sintirin sojoji da wahala ga jami’an tsaro.

“Zai fi alheri gwamnoni su kashe kuɗaɗe wajen ceton rayukan al’umma a maimakon kashe biliyoyi wajen zuwa ta’aziyya.”

“Rai ɗaya ya fi kowanne irin lamari na siyasa,”Abubakar ya faɗa.

A yayin da yake yin martani ga masu sukar yin sulhun, ƙungiyar ta ce sulhu hanya ce da aka gwada a ƙasashe daban-daban kuma ya yi aiki wajen kawo ƙarshen tashe-tashen hankula.

“Hatta ƙashen da ke da ƙarfi sun yi sulhu da mutane kamar Taliban, Al-ƙaeda da Houthis. Yin sulhu ba gazawa ba ce, abu ne da ya shafi ceton rayuka,” ya bayyana.

Sannan ya yi Alla-wadai da wasu gwamnoni waɗanda ke cewa suna da masaniya kan motsin ‘yan ta’adda amma suka gaza bai wa jami’an tsaro wannan bayanan.

“Bai kamata ga shugaba ba ya ce ya san motsin ‘yan ta’adda amma ya gaza ba da wannan bayani. Wannan farfaganda ce da ba ta dace,” ya faɗa.

Haka kuma Abubakar ya kare matakin NSA da al’umma da ke amfani da wannan hanya yana mai gargaɗin kaucewa amfani da siyasa a yayin ƙulla sulhun.

Sannan ƙungiyar ta yaba wa shugaban kwamitin majalisar dattawa kan tattara bayanan sirri, Shehu Buba, da wasu ‘yan Nijeriya da suke aiki wajen tabbatar da an dawo da zaman lafiya a yankin.

“Abin a yaba wa Nuhu Ribado ne saboda manufar da ke tattare da shirin.”

“Duk wani ɗan Arewa mai sanin yakamata akwai buƙatar ya yi na’am da wannan ƙoƙari na kawo ƙarshen zubar da jini da kuma hare-hare marasa iyaka da ‘yan bindiga ke kai wa da sauran abubuwa da ke raba kan al’umma,” ya faɗa.

ƙungiyar ta buƙaci gwamnonin Arewa maso yamma da su yi aiki tare da ofishin NSA da ministan tsaro da manyan hafsoshin tsaro domin tabbatar da nasarar shirin amfani da hanyoyin lumana wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro.

By ukarofi