Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Asusun Tallafawa Illimi na Majalisar ɗinkin Duniya da ƙungiyar ƙasashen Turai tare da haɗin gwaiwar hukumar illimin bai ɗaya ta Jihar Kano sun gudanar da taron gangamin wayar da kai dangane da shirin mayar da yara makarantu a Jihar Kano, da nufin kawo ƙarshen rashin zuwan yara makaranta mai taken “Education And Youth Empowerment Project in Northern Nigeria.
Da take jawabinta yayin buɗe taron wanda aka gudanar a makarantar sakandiren gwamnati dake Gwammaja a ƙaramar hukumar Dala wakiliyar Asusun tallawa illimin yara na Majalisar ɗinkin Duniya Hajiya Aisha Abdullahi ta bayyana cewa maƙasudin shirin shine don ƙara ƙarfafawa iyayen yara, shuwagabanni ƙungiyoyi, ƙungiyoyin mata gwiwa don ganin yara na shiga makarantu a wannan zangon karatu na shekara ta 2025/2026. Dama kara karfafawa mahalarta taron gwiwa wajen tunkarar duk wata matsala dake hana yara zuwa makaranta ko barin makaranta bayan sun fara zuwa.
A cewarta dukkan yara sun cancanci zuwa makaranta “akwai yara da dama da suke ba a makaranta ba saboda rashin wayewa, buƙata ta musamman, bambanci jinsi wanda ke kawo raguwar zuwan yara makaranta, wasu kuma wuraren suna fuskantar matsalar barin yaran daga bayan sun fara zuwa makarantu.”
Ta kuma ƙara da cewa ƙungiyoyi na da muhimmiyar rawar da za su iya takawa wajen shawo kan wannan matsalar “idan aka samu haɗin kai tsakanin ƙungiyoyi da gwamnati hakan zai mutuƙar taimakawa wajen ƙara wayar da kan al’umma musammam iyayen yara, masu kula da su wajen ganin ana sanya idanu dan ganin suna zuwa makarantar akan lokacin kuma a kowace rana.
Babban maƙasudin wannan taron dai shine samun hanyar magance matsalar rashin kai yara makarantu da kuma daina zuwansu daga baya. Dama haɗa kai da ƙungiyoyin iyaye da malamai na makarantu, ƙungiyoyin mata da na masu buƙata ta musammam da nufin farfaɗo da harkar illimi a ƙasar nan musammam ɓangaran Arewacin ƙasar nan wanda ake ganin shine kuma baya ta fannin illimi.
A nasa jawabin wakilin Arewa Alhaji Dalhatu Jibrin godewa irin wadannan kungiyoyi yayi na kasashen wajan ganin yadda suke tiri tiri dan ganin illimi ya farfadu a kasar nan. Inda ya ce matsalar gyaran illimi ba abu ne da ya ta’allaƙa akan gwamnati kawai ba sai an haɗa hannu kuwa ya shigo ciki don magance wannan matsala musammam iyaye,shuwagabannin al’ummar, sarakunan gargajiya, don ganin an ceto wannan fannin daga durƙushewa.
Da yake tofa albarka cin bakin Shugaban majalisar kansilolin karamar hukumar Dala Hon. Auwalu Ibrahim Shu’aibu nuna farin cikinsu ya yi tare da gode wa waɗannan ƙungiyoyi ganin yadda suke tallafawa fannin illimi a wannan jiha. Tare da bada tabbacin majalisar ƙaramar hukumar na bada duk wani gudunmawa daka iya tallafawa don ganin shirin ya ɗore an samu nasarar da ake buƙata.
