Majalisar Wakilai ta gayyaci ministoci kan jinkirin aiwatar da kasafin 2024

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai ya nuna damuwarsa kan yadda kan tafiyar hawainiyar aiwatar da dokar kasafi na shekarar 2024-2025, inda ya gayyaci Ministan Kuɗi, Wale Edun, da ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare na ƙasa, Sanata Atiku Bagudu, domin bayar da bahasi.

An ruwaito cewa, ’yan majalisar sun yi ganawar sirri da ministocin ne a ranar Laraba a Abuja, inda suke neman ƙarin haske kan dalilin da ya sa har yanzu ‘yan Nijeriya ba su ga tasirin kasafin kuɗin ba, duk da irin tabbacin da gwamnatin ta yi.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaman, Shugaban Kwamitin, Abubakar Bichi (APC–Kano), ya ce ‘yan Nijeriya sun damu da yadda ake aiwatar da kasafin kuɗin, musamman yadda ƙasar ke fama da tsadar rayuwa, hauhawar farashin kayayyaki, da kuma dakatar da ayyukan more rayuwa.

“Mun yi hulɗa da Ministocin Kuɗi; dukkansu sun amince da damuwar kuma sun ba mu tabbacin yin aiki tuƙuru domin ‘yan Nijeriya su fara ganin sakamako na zahiri daga kasafin,” inji Bichi.

“Mambobinmu sun damu matuƙa, kuma ministocin sun yi alƙawarin cewa kafin ƙarshen wannan shekarar, ‘yan Nijeriya za su shaida muhimman sauye-sauye da ci gaba, sun ba mu alƙawura, kuma za mu sanya ido sosai.”

Da yake mayar da martani, Ministan Kuɗi Wale Edun ya bayyana cewa ya zuwa watan Satumba na shekarar 2025, an aiwatar da kusan kashi 80 cikin 100 na kasafin kuɗin shekarar 2024.

“Gaba ɗaya aiwatar da shi ya kai kusan kashi 80 cikin 100, kamar yadda kuka sani, Majalisar Dokoki ta ƙara wa kasafin kuɗin 2024 zuwa Disamba, don haka har yanzu ana ci gaba da aiki. Mun kuma sake duba kasafin kuɗin 2025, inda muka mayar da hankali kan ayyukan da za a yi daga tushe da muhimman ababen more rayuwa kamar tituna, ban ruwa, da sauran abubuwan da ke shafar ‘yan Nijeriya kai tsaye,” inji Edun.

Ministan ya dage cewa tattaunawa da ‘yan majalisar sun mayar da hankali ne kan tabbatar da cewa an karkatar da albarkatun kan ayyukan da ke da tasiri sosai. “Musamman, ayyukan da suka shafi tushen ƙasa, wacanda ke ba da tallafi, albarkatu, da kayan aiki kamar aikin ban ruwa da sauran ayyukan more rayuwa a matakin ƙasa, an ba su cikakkiyar kulawa da fifiko.”

Dangane da damuwa game da karin kashe kuɗi, Edun ya fayyace cewa “babu wata tattaunawa kan ƙarin kasafin kuɗin 2025.”

A nasa ɓangaren, ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare na ƙasa, Sanata Atiku Bagudu, ya bayyana cewa ‘yan majalisar sun yaba da nasarorin da gwamnatin ta samu da kuma kyakkyawar alaƙar aiki da majalisar ta ƙasa.

By ukarofi