Nijeriya ta daɗe tana fama da gurɓatattun shugabanni – Sarki Sunusi

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa Najeriya ta daɗe tana fama da shugabanni marasa inganci waɗanda ba su da hangen nesa. Sanusi ya ce wannan rashin sa’a wajen samun shugabanni nagari shi ne babban dalilin da ya sanya ƙasar ke fama da matsaloli na tsawon lokaci.

Sanusi ya yi wannan jawabi ne a yayin bikin Kano International Poetry Festival (KAPFEST) karo na biyu da aka gudanar a Kano, ƙarƙashin ƙungiyar Poetic Wednesdays Initiative (PWI). Ya ce shugabanci mai kyau shi ne ginshiƙin ci gaban kowace ƙasa, kuma dole ne Najeriya ta daina ɗaukar shugabanni da basu da kishi.

A cewarsa, idan ba a cire tallafin mai da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi ba, Najeriya da yanzu ta shiga mawuyacin halin karyewar tattalin arziki. Ya bayyana cewa tallafin da ake kashewa a baya ya fi amfani wa ƙasashen Turai wajen buɗe masana’antunsu, yayin da Najeriya ba ta amfana da komai ba.

Sanusi ya kuma soki yadda gwamnati ke ci gaba da ciwo bashi marar amfani, yana mai gargaɗi cewa irin wannan dabi’a za ta haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin ƙasa a nan gaba. Ya ce dukiya mai tarin yawa da ake ɓatarwa a kan batutuwan banza da kuma rarrabuwa tsakanin ƙabila da addinai suna ƙara janyo koma-baya.

Sarkin daga ƙarshe ya buƙaci matasa su tashi tsaye domin karɓar shugabanci daga hannun tsofaffin ‘yan siyasa. Ya ce da azama da kishin ƙasa, matasa za su iya jan ragamar mulki da kawo sauyi mai ɗorewa a Najeriya. Sanusi ya ƙara da cewa lokaci ya yi da za a daina dogaro da tsofaffin da suka daɗe suna jagorantar ƙasa ba tare da ci gaba ba.

A nata jawabin shugabar ta PWI, Nasiba Babale, ta ce taken taron na bana “Poetry in a Time of Crisis” na nufin tunatar da mawaƙa da masu fasaha muhimmancin amfani da kalmomi wajen yaɗa zaman lafiya musamman a Arewa mai fama da rikice-rikice.

By ukarofi