
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano ta ƙara azama wajen faɗakar da al’ummarta muhimmancin rijistar katin zaɓe da ake cigaba da gudanarwa a halin yanzu a faɗin Nijeriya.
Hakan ya samu ne a sakamakon jajircewa da aiki tuƙuru na shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, kamar yadda wasu daga cikin al’umar yankin suka bayyana.
A zantawar da jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta yi da wasu daga cikin al’ummar yankin a Mazaɓar Hagagawa, da dama sun bayyana farin cikinsu ganin yadda aka wayar musu da kai kan muhimmancin mallakar katin.
“Duk wanda bai yi rijistar katin zabe ba, ya je ya yi saboda shi ne zai nuna masa cewar ya san kansa kuma ya san me yake yi, saboda an ce kuri’arka ‘yancinka”, inji wani Musa Abdullahi Shamaki a zantawarsu da ita.
“Shi wannan kati shi ne yake canja rayuwar al’uma daga wani matsi zuwa wani mataki wanda yake na sauki”, inji Mansur Abdullahi Mukaddas.
Alhaji Hamza Mai Fata ya bayyana hoɓɓasan a matsayin abinda ya haifar da ɗa mai ido, musamman a fannin haɗa kai da masu riƙe da sarautu a dukkan harkokin jama’ar yankin.
A nasa bangaren, Sakataren Hakimin Bichi, Malam Idris Shitu Malikawa, wanda ya yi jawabi a madadin Hakimin Bichi kuma Galadiman Kano, Alhaji Mannir Sunusi, ya ce masu riƙe da sarautu a yankin suna ba da cikakken haɗin kai da goyon baya wajen faɗakar da al’umma.
“Kullum muna ba da shawara cewa mutane su fita su jaddada katin zaɓe, duk wanda ya kai shekara 18 ya yi ƙoƙari ya je kafin a rufe fotal ɗin ya yi”, inji shi.
Ya kuma ci alwashin cigaba da bayar da dukkan gudunmawar da ake buƙata domin cimma nasarar da aka sa gaba.


