AGILE ta wayar da kan wakilan kafafen yaɗa labarai kan ilimin mata a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ma’aikatar ilimi ta jihar Zamfara tare da haɗin gwiwar hukumar AGILE a yau Lahadi sun gudanar da taron wayar da kai ga kafafen yaɗa labarai da nufin inganta tsarin ilimin yara mata a jihar.

A jawabin maraba shugabar shirin AGILE ta jihar Sa’adatu Abdu Gusau ta bayyana cewa taken shirin shine “ci gaban sadarwa ga matasa”

Ta jaddada buƙatar ’yan jarida dake aiki a Jihar su ba da muhimmanci sosai kan ilimin yara mata a rahotonsu a jihar.

Ta ci gaba da cewa, maƙasudin taron shine don ƙarfafa aikin yaɗa labarai kan hanyoyin sadarwa na ci gaba, don inganta haɗin gwiwa a cikin rahotanni da kuma ayyukan da ake yi don inganta Ilimi da ƙarfafawa Matasa a jihar, da samar da bayanai da fadakarwa kan shirye-shiryen da suka shafi ilimi don ƙara yawan sanya ƴaƴa mata a makaranta.

A cewarta, a shekarar da ta gabata , shirin na AGILE a jihar ya tallafawa tsarin kula da harkokin ilimi wajen gudanar da ƙidayar ɗalibai a duk shekara wanda ya nuna an samu ƙaruwar ɗalibai 115,470.

Ta ƙara da cewa aikin na AGILE ya inganta yawan masu rajista daga 854,990 a shekarar 2023 zuwa 905,323 a shekarar 2024 wanda hakan ya yi matukar raguwar yara 155,503 da ba sa zuwa makaranta.

Ta kuma bayyana cewa, an horar da malaman kwamfuta 103 daga makarantun sakandare 50 don koyon ilimin kwamfuta a ƙarƙashin wannan aiki.

Hajiya Sa’adatu ta ci gaba da bayanin cewa a ƙarƙashin aikin an sayo na’urorin kwamfuta 1,100 da na’ura mai ɗaukar hoto 50 da kuma allunan majigi 50 don bunƙasa ilimin zamani.

Ta kuma buƙaci masu aikin yaɗa labarai a jihar da su riƙa wayar da kan jama’a musamman iyaye a kan muhimmancin sanya ‘ya’yansu mata makaranta don samun nagartaccen zuriya masu zuwa.

By ukarofi