Daga ALI ABUBAKAR SADIK
Allah ya jiƙan Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi, saboda irin kyakkyawar niyyarsa wajen kafa Izala, domin farfaɗo da ilimin addinin Musulunci tsakanin al’ummar Musulmin Nijeriya. Kamar yadda marigayin a wata hira da ya yi, wacce ya nuna, tunanin kafa wata ƙungiya a Nijeriya wadda za ta yi wannan aiki ya samo asali a shekarar 1962 lokacin aikin hajji na wannan shekarar.
Sheikh Gumi da Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello, an ba su masauki a gidan saukar baƙi na Abdallah Khalid da ke Mina kusa da Jamra (wajen jifan shaiɗan). A wajen jifan shaiɗan ɗin, sai Gumi ya ga alhazan Nijeriya na dukkan Jamra da takalmi da yin tsinuwa, zatonsu ko shaiɗan ɗin ne a wajen. Wannan abin kunya a addinance ya ɓata ran Gumi sosai wanda ya nuna takaicinsa ga Sardauna. Sai Sardauna ya tambaye shi mene ne mafita? Sai ya ba shi amsar cewa, “dole a koma a karantar da mutane Ilimi.” A wannan lokaci Sardauna ya na bayar da kuɗaɗe ana gina masallatai a wurare daban-daban na Arewa, wanda Gumi ya yi masa tambayar cewa, “mene ne amfanin gina masallatai ga jakuna?” Manufa dai Musulmin da ba su san hukunce-hukunce na addininsu ba irin waɗannan masu duka, maimakon jifan sheɗan, na da buƙatar Ilimi fiye da masallaci.
Gumi da Sardauna sun nemi tallafin ƙasashen Saudi Arabia da Kuwait, domin gina masallacin Sultan Bello da wata cibiya da za ta yi wannan aiki. Bayan dawo wa Nijeriya an kwafa kwamiti, wanda ya bayar da shawarar kafa Jama’atu Nasril Islam (JNI), wacce ta yi daidai da manufar Sardauna ta siyasa, domin ya na da nufin kafa ƙungiya, wacce ya kira Usmaniyya (wato alaƙa da ɗan Fodio kenan ko?), wadda za ta haɗe kan Musulmin Nijeriya gabaɗaya. Domin a wannan lokaci, rikici tsakanin ’yan Tijjaniyya da ’yan ƙadiriyya ya ɗauki salon siyasa yadda Tijjaniyya ta yi ƙarfi sosai a Kano ƙarƙashin jagorancin Muhammad Sunusi I, kuma ya ke amfani da wannan iko wajen yi wa Sardauna gani-gani, abinda a ƙarshe ya janyo masa cajin cin hanci da ‘Muffet Commission’ suka yi masa. wanda ya tilasta shi yin murabus. Bugu da ƙari kuma, Sarkin Musulmi, wanda ke bin ɗarikar ƙadiriyya na kallon duk sarkin da ya rungumi Tijjaniyya yana barazana gare shi, abinda a baya ya janyo aka tsige Sarkin Zazzau sakamakon bayyana karɓar Tijjaniyya. Sannan kuma da rikicin da ya ɓarke a Argungu tsakanin ’yan wazifa da ’yan ƙadiriyya sakamakon saɓanin ƙablu da sadlu cikin shekarar 1965.
To, a ƙoƙarin kawo daidaito da haɗin kan Musulmi, Gumi da Sardauna sun nemi kafa JNI da tallafin da su ka samu daga ƙasar Saudiyya (kimanin 250,000 Sterling Pounds) da kuma Kuwait (200,000 Sterling Pounds), wanda aka gina masallacin Sultan Bello, cibiyar JNI a titin Ali Aƙilu da Kwalejin Sardauna Memorial College da kuma sauran ayyuka na da’awa a ƙarƙashin JNI akwai malamai daga kowane ɓangare na ƙungiyoyin Musulmi. Akwai su Sheikh Gumi (Izala), Nasiru Kabara (ƙadiriyya), Shehu Mai Hula (Tijjaniyya), Sa’id Hayatu (Mahdiyya) da waɗanda ba sa tare da wata ƙungiya irinsu Shehu Galadanci da Halliru Binji.
Da tafiya ta yi tafiya, rikici ya samo asali a lokacin da wasu cikin JNI suka fara zargin cewa, Gumi ya na karkatar da kuɗaɗe (amma fa ba a aljihunsa ba) zuwa wasu wurare da ba JNI ba, domin a lokacin shi kaɗai Saudiyya ta yarda da shi, kuma ita ke bai wa JNI tallafi mafi tsoka. Su kuma Saudiyya, sanin kowa ne cewa, kuɗaɗensu na yaɗa Salafanci/Wahabiyanci ne kawai.
Rarrabuwa tsakanin malaman JNI ya kai maƙura ne a 1971 lokacin da bayan saukar Abubakar El-Nafaty daga shugabanci, maimakon a bai wa Na’ibi Suleiman Wali, wanda shine mataimakinsa, sai Gumi ya ɗaure gindin aka bai wa abokinsa Ibrahim Dazuki. Wannan ya sa malaman Kano suka fusata da cewa, ashe abin siyasar Sakkwato ake, ba Musulunci ba. Wannan shi ya ruguza JNI yadda ba ta yi tasirin da aka so wajen haɗe kan Musulmi ba. Magajiyarta, Majalisar ƙoli Ta Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA), wacce aka ƙirƙira a 1973, ba ta iya cike wannan gurbi ba, domin ita ma sai ta haɗe kai da Rabita (ta Saudiyya), ko da yake ta yi nasara guda ɗaya a ganinta, wato na soke ƙungiyar Ahmadiyya da kafirta ayyukanta a Nijeriya.
Da ma tun kafin watsewar haɗin kan JNI, an zargi Gumi da karkatar da kuɗaɗenta. Da alamu dai sabuwar ƙungiyarsa ta Izalatul Bid’a Wa Iƙamatus Sunna ya riƙa karkatar da kuɗaɗen. Kasancewar sa daga Sakkwato, asali Gumi ɗan ƙadiriyya ne, dalilin da ta su ta zo ɗaya da Malam Nasiru Kabara a yayin zaman ɗalibtarsa a Kano, inda ya halarci makarantar SAS, kuma Nasiru Kabara ya kasance malaminsa. A Kano ɗin dai ya saba da babban malamin Mahdiyya, wato Sheikh Sa’id B Hayatu (wanda ake kira da Baba Ansar’en), wanda suka yi ɗalibta a gabansa da mahaifina, wato Abubakar Malam Fari. Gumi ya auri ’yar Sa’id Hayatu, wato Maryamu. Haɗuwar Gumi da Malam Aminu Kano tun a Maru, inda suka riƙa tattaunawa game da yadda addini ya cakuɗu da al’ada, na cikin ginshiƙin abinda ya saita tunanin Gumi wajen ƙoƙarin kawar da bidi’a da aiki da sunna. Kuma waɗannan mutane da ya haɗu da su a Kano ya daɗa ba shi damar ƙoƙarin yakice al’ada ta amfani da ilimi (Intellectual). Wannan tarbiyya ita ta haifar da kafa Izala, kuma mu’amalarsa da Sardauna da mutanen Saudiyya ta ba shi Iko na siyasa (political) da tattalin arziki (economic). Izala ta kafu a ƙarƙashin jagorancinsa a shekarun farko ta 1970.
Kuskuren Gumi, a wajena da wasu da dama, shine gazawarsa wajen bin kundin tsarin wa’azi, kamar yadda Allah ya umarta cewa; ƙ16:125 “Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa’azi mai kyau kuma ka yi jayayya da su da magana wacce take mafi kyau. Lallai ne Ubangijinka Shine Mafi sani ga wanda ya ɓace daga hanyarSa, kuma Shine Mafi sani ga masu shiryuwa.”
Wato dole mai wa’azi ya yi koyi da wannan ayar, da yadda Annabi Muhammad (SAW) da Annabi Ibrahim (AS) suka yi wa’azi da hikima da maganganu masu kyau. Misali da Annabi Ibrahim ya karya gumaka, da aka rutsa shi me ya ce? Sai ya ce, su tambayi babban gunki. Ka ga wannan shine hikima, domin za su gane wautar bautar abinda bai iya kare kansa ko yin magana. Shi kuma Annabi Muhammad lokacin da ya fito daga ɗa’if an yi masa rotse, me ya ce? Sai ya yi musu addu’ar shiriya. Wannan shine magana mai kyau, wato sassauci ko ga kafiri.
To, amma Gumi tun a Maru, lokacin rigimarsa da Sarkin Musulmi kan limaminsu mai yin taimama, wanda a ilimance ya nuna kuskurensa, wataƙila domin neman ramuwa akan Sarkin Musulmi, sai ya bayar da fatawar cewa, karɓar lambar girmamawa ta ‘KBE’ daga hannun Turawan Ingila da Sultan ya yi Kafirci ne. Wannan ya nuna rashin bin ƙa’idar wa’azi, wanda haka Wahabiyanci ya gado kuma da haka Izala ta ginu akan sa a wannan ƙasa. Wato duk abinda ya saɓa da fahimtarsu, sai su ɗora maka kaulasan, abinda ake kira da “Takfir” a tsarin da’awar Wahabiyanci.
Ko da yake, zuwan Izala ya kawo canji mai alfanu ta fannoni daban-daban. Misali; yaɗuwar ilimi, wanda Gumi ya gaya wa Sardauna tun a 1962, sannan ya ’yantar da mata wajen neman Ilimi da shigo wa al’umma a dama da su, ya kuma kawo karɓar Boko da aikin banki da shiga siyasa, inda maganarsa ta cewa, zaɓe ya fi sallah, wacce a wancan lokacin ta yamutsa hazo, sai a yanzu mutane ke gane falsafa da gaskiyar maganarsa. To, amma zuwan Izala, saboda rashin iya wa’azi, ya janyo ƙarin rarrabuwar kawunan Musulmi fiye da a baya. Ya janyo lalacewar tarbiyya tsakanin manya da yara, sannan ya kawo harkar son abin duniya ga akasarin malamai, saboda irin tallafin kuɗaɗen waje da ke shigowa da su da sunan ƙungiya. Wannan ya daɗa jefa malamai wajen kusantar mahukunta da ba su fatawoyin son rai, domin abin duniya. A kullum idan na tuna malaman Izala, Ina tuna lokacin rikicin Gandollar, lokacin da Sheikh Sale Pakistan ya jagoranci malaman Izala zuwa gidan Gwamnatin Jihar Kano kuma a rediyo ya ke cewa, “yadda Allah ya wanke Aisha daga zargin zina, haka suke sa ran zai wanke Ganduje daga zargin cusa Dala”.
Rashin kunya tsakanin malamai ya daɗa ƙaruwa matuƙa, sannan gaba tsakanin Musulmi da Kiristoci ta daɗa ta’azzara baya ga duk inda ka sami ’yan ta’adda masu tsaurin ra’ayi, za ka samu gyauron Wahabiyawa ne (Boko Haram, ISWAP, ISIS, Shabab da sauransu). Don haka lokaci ya yi da malaman Izala za su canza akalar yadda suke yin wa’azi, domin yanayin wa’azinsu, maimakon haɗin kai, a kullum ƙara farraƙa Musulmi ya ke yi, kuma tun daga majalisin Gumi aka fara samun irinsu Sheikh ɗangungu, wanda almajirin Gumi ne kafin ya fanɗare masa da a yanzu kuma aka sami irinsu Masussuka ke far musu. Haka nan salon wa’azin Izala ne ya ƙarfafi Shi’a a ƙasar nan yadda kusan gidan kowa akwai a yanzu. Hatta yadda wasu matasan ’yan boko ke shiga Mulhidanci, ya samu gagarumin tasiri da yadda malaman Izala ke wa’azi, kuma ba za mu manta da yadda babban ɗan marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ya karɓi wannan aƙida ta Mulhidanci ba. Duk waɗannan abubuwa yanayin wa’azin Izala ya assasa su.
Niyyarsu Gumi wajen samar da ilimi da wayar da kan Musulmi da kuma bin addini kan shari’a niyya ce mai kyau, amma aka ɓata ta da yadda ake ƙoƙarin isar da ita ga al’umma. Don haka ƙalubalen malamai, ba na Izala kaɗai ba, shine komawa ga ginshiƙin wa’azi kamar yadda Allah ya umarta a waccan ayar ta sama. Ta haka ne kaɗai za a iya samu haɗin kan Musulmi, kuma a zauna da waɗanda ba Musulmi ba cikin amana. Mun dai ga yadda rashin haɗin kan Musulmi ke ta kassara mu ta kowace fuska a halin da ake ciki yau a Nijeriya da duniya.
Shin ko ƙoƙarin baya-bayan nan na Sheikh Maƙari wajen sake farfaɗo da haɗin kai tsakanin malamai duk da bambancin aƙida zai yi tasiri kuwa? To, abin kamar da wuya, amma dai lokaci ne kaɗai zai tabbatar. Kar dai mu manta da umarnin Allah cewa; “Fa’atasimu bi hablillahi jami’a, wa la tafarraƙu”!!!
