Lamarin ’yan bindiga ya fara wuce gona da iri yayin da ake ƙorafin suna karɓar haraji kafin a birne mamaci.
Wasu shugabannin al’umma a Lilu da Agwa da ke jihohin Anambra da Imo ne suka yi wannan ƙorafi.
Shugabannin sun bayyana haka ne a yayin gabatar da rahoton ‘Amnesty International’ a kan kisan gilla a Kudu maso Gabas a Ikeja, Legas.
Al’ummomin sun koka cewa ana tilasta wa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu biyan kuɗin harajin birne mamata ga yan bindiga.
Sakataren fada na Lilu, Dr. Dominic Okoli, ya bayyana cewa tsakanin 2020 zuwa 2025, an kashe mutum 25 sannan an lalata gidaje fiye da 30.
Okoli ya bayyana cewa al’umma na fuskantar matsala ta kiwon lafiya, makarantu sun tsaya, kuma mahara suna karɓar kuɗi kafin a binne mamata.
Ya ce, “Mu na son birne mamatanmu, amma kafin ka birne mamaci dole sai ka je ka nemi izini daga yan bindiga, a kuma biya su kuɗi.”
A na shi ɓangare, Nduka Ozor daga Agwa ya tabbatar da cewa ana tilasta biyan kuɗin binne mamata, wanda a wasu lokuta zai kai N500,000.
Ya ce, an kashe mutane da dama ciki har da Sarki, ɗan uwansa, da mace mai ciki, kuma duk maharan a bayyane suke yi babu rufe fuska.
Ya yi kira ga jami’an tsaro da shugabanni su taimaka, yayin da ‘Amnesty International’ ta bukaci gwamnati ta bincika kisan gilla a Kudu maso Gabas.
Rundunar ’yan sanda a Anambra ba ta amsa tambayoyi game da lamarin ba, yayin da hare-haren suka ci gaba da ta da hankalin jama’a da masana.
A watan Yuli da Agusta, mutum 12 aka kashe a wasu al’ummomi a Imo, yayin da aka sace yara uku a Amansea, Anambra.
Rahoton ya bayyana cewa an kashe ɗaya daga cikin yaran bayan ya ki bin umarnin masu garkuwa da shi kan ɗabi’ar da suka buƙata.
