Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Matatar man Dangote ta ƙaryata labarin shirin rufe sahen matatar man fetur na tsawon watanni biyu zuwa uku.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, za a iya rufe sashin mai a matatar Dangote na tsawon watanni biyu zuwa uku domin gyara.
Kamfanin dillancin labaran na ƙasa da ƙasa ya nakalto daga shafin sa ido na kamfanin IIR Energy cewa zai yiwu a rufe sashen mai da ke da ƙarfin tace ganga 650,000 a kowacce rana tun a ranar 29 ga watan Agusta bayan da aka samu tsaiko.
Rahoton ya ƙara da cewa, matatar ta shirya yunƙurin sake kunna sashin Residue Fluided Catalytic Cracking Unit mai tace ganga 204,000 a ranar 20 ga Satumba, amma manyan gyare-gyare da maye gurbin kayan aiki na iya sanya rukunin a rufe shi na tsawon watanni.
Sai dai mai magana da yawun rukunin Dangote, Anthony Chiejina, ya bayyana rahoton a matsayin “aarya”.
“Labarin ƙarya. Me ya sa ake yaɗa wannan labari?” Chiejina ya shaida wa jaridar Punch lokacin da aka tuntuɓe shi don jin ta bakinsa a ranar Lahadi, 7 ga Satumba, 2025.
Matatar mai ta Dangote da ta fara sarrafa ɗanyen mai a watan Janairun 2024, ta kawo cikas ga cinikin man fetur daga Turai zuwa Yamma.
Man Fetur da Tarayyar Turai da Birtaniya ke fitarwa zuwa Nijeriya sun ragu daga matsakaicin kusan ganga 200,000 a shekarar 2024 zuwa kusan 120,000 a farkon rabin wannan shekarar, a cewar bayanai na Kpler.
