Gwamnatin Katsina ta ɗauki mutane 35,903 aiki

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin shirin ta na inganta makomar al’ummar Katsina ta ɗauki mutane 35,903 aiki a fanni daban daban.

Sun haɗa da ɗaukan malamai na makarantar firamare da na sakandare,masu unguwanni, jami’an tsaro na CWC da ‘yan banga.

Akwai kuma yan sa kai,mafarauta,da malaman addini.

Mataimakin gwamnan jihar Farouk Lawal joɓe ya sanar da haka a wajan taron masu ruwa da tsaki da suka haɗa da sarakunan gargajiya, manyan jami’an gwamnatin tarayya da na jiha, manyan ƴan kasuwa malamai yan asalin jihar.

Taron wanda gwamnatin jihar Katsina ta shirya, gabatar da aikace-aikacen da ta aiwatar fannin daban-daban har da matsalar tsaro da ya addabi jihar.

Kamar yadda mataimakin gwamnan ya ce, gwamnatin Dikko Raɗɗa ta kashe kuɗi Naira biliyan 74.96 wajen gina hanyar shatale tale mai tsawon kilomita 24 da gina wasu tagwayen hanyoyi a garin Katsina.

“Gwamnatin jihar ta kuma gyara wasu hanyoyi a shiyar Funtua da Daura,”inji Joɓe.

Ya taɓo fannin ilimi, lafiya,noma da ruwan sha da gwamnatin ta aiwatar da aikace-aikace a kai.

Malam Joɓe ya bayyana cewa gwamnati ta kashe Naira biliyan 24 wajen biyan ma’aikata kuɗaɗen su na ajiye aiki(Gratuities) da biyan sabon tsarin albashi da tallafawa lokacin azumin Ramadan.

Shima da yake gabatarwa masu halartar taron halin da ake cikin kan yanayin tsaro a jihar, kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya bayyana musabbabin ta’addanci a jihar da matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka da kuma yanayin da ake ciki yanzu .

Ya bayyana cewa gwamnati ba ta da hannu a sasancin da ke wakana a tsakanin ƴan bindiga da wasu ƙananan hukumomi.

“Al’ummar ƙananan hukumomin ne da su ƴan bindigan suka buƙaci haka,ita dai gwamnatin jihar ta kan taimakawa waɗanda hare haren yan bindiga a shafa,”Dr Ɗanmusa ya ce.

A nasa jawabin gwamna Dikko Raɗɗa ya ce yana maraba da suka mai ma’ana kuma ƙofar sa a buɗe take wajen karɓar shawarwari.

Ya kuma bayyana ƙudirin tunkarar matsalar tsaro da jajircewa wanda yace dama shi ya fara ambata a lokacin da ya ke gabatar da ƙudurorin sa ga al’ummar jihar tun lokacin da yake gabatar da yaƙin zaɓe.

Tsohon gwamna Rt Hon Aminu Bello Masari da Sarkin Daura Farouk Umar Farouk da Wazirin Katsina Sanata Ibrahim Ida na daga cikin waɗanda suka halarci taron.

Saura sun haɗa da ministan Gidaje Musa Dangiwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsare-tsaren gwamnati Hadiza Bala Usman.

Akwai su sanata Abu Ibrahim, sanata Hadi Sirika da Dahiru Barau manual da kuma tsohon shugaban hukumar DSS Lawal Daura.

Haka kuma akwai tsarin manyan sojoji da sauran jami’an tsaro ƴan asalin jihar a wajen wannan taro.

By ukarofi