Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Tsohon kwamandan hukumar yaƙi da ‘yan ta’adda ta Zamfara Bello Muhammed Bakyasuwa ya maka ƙaramin ministan tsaro, Bello Muhammad Matawalle da wasu yaranshi tare da ƙafar yaɗa labarai DCL Hausa a babbar kotun birnin tarayya Abuja bisa abin da ya bayyana na ɓata masa suna.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma ya gabatar ga manema labarai a yau Litinin a Gusau.
Bakyasuwa, ƙwararre kan harkokin tsaro, kuma jami’in soja mai ritaya, ya bayyana matakin da Matawalle da yaran suka ɗauka a kansa a matsayin wani yunƙuri na zubar masa da kima.
“Ina jan hankalin Matawalle da ‘yan siyasarsa kan maganganun ƙarya da su kayi da cewar zarginsu a kaina ba shi da tushe.” Yace.
Ya zargi Hon Bello Muhammed Matawalle, ƙaramin ministan tsaro, da yaransa Anas Abdullahi Ƙaura, Sani Nasiru Makari, Aliyu Alhazai Shinkafi da yin hira da DCL Hausa inda suka faɗi miyagun kalamai a kansa.
A cewarsa, matakin da yaran Matawalle suka yi masa wani yunƙuri ne na cutar da mutumcinsa, yana mai alanƙanta shi da tsagwaron siyasa.
Ya bayyana cewa tuni kotun ta gayyaci dukkan waɗanda ake tuhuma biyar yanzu haka a babbar kotun birnin tarayya Abuja.
“Ina neman haƙƙina kotu bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya kan yadda suka yimin ƙazafi da ɓata min suna”.
Bakyasuwa wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Maradun, mahaifar ƙaramin ministan tsaro Hon Bello Mohammed Matawalle ya bayyana cewar ba zai fasa yin sharhi dangane da Matsalar rashin tsaro da Jihar Zamfara take fuskanta ba.
Kamar yadda nake faɗa a kullum, a matsayina na ɗan asalin Jihar Zamfara, ba zan yi shiru ba yayin da al’ummarmu ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane a kullum.” Inji Bakyasuwa.
