‘Yan sanda sun kama muggan makamai cikin wata mota a Zamfara

Spread the love

‘

Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta kama bindigogi AK-47 guda huɗu, alburusai 228 da magazin huɗu a lokacin sintiri a kan titin Gummi–Sokoto. Jami’an sun tare wata mota ƙirar Toyota Corolla da ke ɗaukar fasinjoji daga Sokoto zuwa Gummi.

Jawabin hakan ya fito ne daga jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Yazid Abubakar a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Sanarwar ta bayyana cewar an gano makaman a cikin jaka mai ɗauke da lemu mallakin wani mutum mai suna Nasuru Dawan Jiya.

Yayin gudanar da bincike wanda ake zargin ya amsa cewa yana jigilar makaman ne domin kai wa ‘yan bindiga da ke aiki a ƙauyen Gurusu.

Makaman sun haɗa da alburusai na PKT guda 200, na AK-47 guda 28 da kuma magazin huɗu ba tare da harsasai ba.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Zamfara, CP Ibrahim B. Maikaba, ya tabbatar wa jama’a da cewa ana ci gaba da bincike don cafke sauran abokan hadadar Wanda ake zargin .

Ya kuma nanata ƙudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.

By ukarofi