‘
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Aƙalla masu Masallata sama da 40 ne aka sace a lokacin da suke gudanar da sallar asuba a yau Litinin a ƙauyen Gidan Turbe da ke ƙaramar hukumar Tsafe a
Zamfara.
Yan ta’addan sun mamaye ƙauyen da yawan su ya haura ɗari dauke da muggan makamai.
Harin dai na zuwa ne sa’o’i 24 da yin sulhu da ‘yan bindigar da ke jihohin Katsina da Zamfara.
Malam Jamilu Lawal Tsafe ya shaidawa Blueprint Manhaja ta wayar tarho da yammacin yau cewa ‘yan ta’addan sun kewaye masallacin ne da misalin ƙarfe 5:30 na safe a lokacin da alummar ke gudanar da sallar asuba .
Sai dai, Zagazola Makama, ƙwararre kan yaƙi da ta’addanci a tafkin Chadi, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun yiwa Masallatan kawanya da bindigogi inda suka tilastawa da dama daga cikin su fita daga masallacin kafin daga bisani sukayi awon gaba da su zuwa cikin daji.
Rahotanni sun nuna cewa waɗanda aka yi garkuwa dasu, ƴanbidigar sun nufi hanyar Gohori da ke Tsafe, inda nan ne maɓoyar kungiyoyin ƴan’ta’addan ke da zama ƙarƙashin jagorancin riƙaƙƙen ɗan ta’addan nan Adamu Aleru.
