Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta gabatar da ƙudurin gaggawa zuwa ga majalisar zartarwa, domin bada tallafi da taimako ga al’ummar Zango, Kankia da Safana, tare da sauran waɗanda ambaliyar ruwan sama ya shafa.
Ɗan majalisa Rt. Hon. Tasi’u Musa, tare , Rt. Hon. AbdulJalal Haruna Runka na Safana da Hon. Salisu Hamza da ke wakilan Ƙananan hukumomin Zango, Safana da Kankia, suka gabatar da wannan ƙuduri. Sun buƙaci majalisar da ta roƙi gwamnatin jihar da ta kai agajin gaggawa ga mazauna yankunan da abin ya shafa.
Haka kuma majalisar ta yi wani ƙuduri na neman gwamnati ta gaggauta magance matsalar zaizayar ƙasa da matsalar hanyoyin ruwa a wasu unguwanni, ciki har da Sabon gida–Unguwar Masoya Annabi–Kwaɗo da Rahamawa a cikin Katsina, da kuma Tawalala–Rahamawa–Bayan Garkar Ambaru–Hanyar Gara/Rimi a ƙaramar hukumar Daura.
Ƙudurin ya kasance na haɗin gwiwa da Kakakin Majalisar, da kuma Hon. Ali Abubakar Albaba, wanda ke wakiltar Katsina.
Sun buƙaci gwamnati da ta tashi tsaye wajen taimakawa al’umman waɗannan unguwanni, domin su kan shiga mawuyacin hali duk lokacin da aka samu ruwan sama.
An bayyana cewa gyaran hanyoyin ruwa da ɗaukar matakan gaggawa zai kawo sauƙin rayuwa ga mazauna wuraren.
Dukkanin ƙudurorin sun samu cikakken goyon bayan yan majalisar, inda Kakakin majalisar Rt Hon Nasiru Yahaya Daura ya bayar da umarnin a miƙa su ga ɓangaren zartarwa domin ɗaukar matakan da suka dace.
