Kotu ta ƙi amince wa buƙatar Nnamdi Kanu ta koma wa Asibitin ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A jiya Litinin Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta soke buƙatar da mai fafutukar kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu ya nema domin ba shi izinin ficewa daga hannun hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) zuwa Babban Asibitin ƙasa don matsalar lafiyarsa ta gaggawa.

Mai Shari’a Musa Liman, wanda ya yi hukunci kan takardar buƙatar ya ce wa’adinsa na gajeren zango a matsayinsa na Alƙali a kotun ya ƙare a ranar, don haka ba shi da hurumin yin hukunci akan al’amarin.

Saboda haka ya umarci a mayar da shari’ar zuwa ga kumdin ƙararraki domin bai wa alƙalin alƙalai damar naɗa wani alƙali da zai yi saurari shari’ar tare da yanke hukunci.

Yayin da aka gabatar da ƙarar, lauyan Kanu ya ce tun a ranar 1 ga watan Satumba aka shigar da ƙorafin yayin da aka miƙa wata takarda da ke inkarin buƙatar daga gwamnati a kotun.

Lamarin da ya sa ya nemi a daga sauraren ƙarar domin ya samu damar duba takardar da kuma la’akari da tafiyar alƙalin.

Da yake tsokaci akan haka Mai Shari’a Liman, ya umarci a miƙa takardar ga kundin domin miƙa lamarin ga wani alƙali, inda ya kuma ce zai tabbatar an gaggauta yin aiki a kai kasancewar batun yana da alaƙa da lafiya.

By Babaji