
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fraministan Isra’ila Pedro Sanchez ya kirayi hukumomin wasanni na ƙasa-da-ƙasa da su haramta wa Isra’ila cigaba da gudanar da harkokin wasanni kamar yadda aka yi wa Rasha a 2022 kan matsa lamba wa Ukraniya.
Da yake jawabi a taron jam’iyyarsu ta ‘Socialist Party’ a ranar Litinin, Sanchez ya ce cigaba da damawa da Isra’ila a harkokin duniya bai dace da cin ƙare babu babbaka da take yi wa Falasɗinawa ba.
Akan haka ya ce, akwai buƙatar hukumomin wasanni su sake nazari game da ko barin ƙasar shiga sahun sauran ƙasashe a lamuran wasanni ya yi daidai da tsare-tsarensu da yaƙar Gaza da take yi.
Ya kuma ƙalubalanci hujjar da ta sa aka haramta wa Rasha shiga wasanni akan faɗanta da Ukraniya amma kuma ake damawa da Isra’ila, yana mai cewa sai an hana Rasha da Isra’ila sannan aka yi adalci.
Kalaman nasa na zuwa ne ƙasa da kwana biyu da masu goyon bayan ƴancin Falasɗinawa suka ƙaddamar da zanga-zangar hargitsa wani gasa na keke da tawagar Isra’ila ke ciki, wadda ake gudanarwa a Birnin Madrid.
Lamarin da ya haɗa su da ƴan sanda, inda aka raunata wasu mutane 22 da kama wasu biyu.
A makon da ya gabata Ministan Wasanni na Sifaniya, Pilar Alegria ya ce ya kama a dakatar da tawagogin wasanni na Isra’ila kamar yadda aka yi wa na Rasha a 2022.
