Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ta raba jimillar Naira biliyan 330 ga magidanta miliyan 8.1 a faɗin Nijeriya a ƙarƙashin shirin tallafin kuɗi (National Social Safety Net Programme), wanda aka ƙirƙiro domin rage wa marasa galihu raɗaɗin sauye-sauyen tattalin arzikin ƙasar.
Ministan Kuɗi kuma Ministan Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Wale Edun, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, bayan wata ganawa da Kwamitin Musamman na Shugaban ƙasa kan ɗaukar nauyin Jinƙai, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa a watan Fabrairu.
Edun ya bayyana cewa shirin, wanda ya fuskanci jinkiri a farkon shekara, yanzu ya dawo sakamakon la’akari da nasarar da aka samu na shigar da bayanan Lambar Shaidar ɗan ƙasa (NIN) ga waɗanda za su ci gajiyar shirin.
Ya ce wannan haɗakar bayanan ta taimaka matuƙa wurin tabbatar da gaskiya da rufe hanyoyin zamba, da kuma kawar da katsalandan na siyasa a cikin shirin.
A cewar Ministan, daga cikin gidaje miliyan 19.7 da aka tantance a cikin rajistar jinƙai ta ƙasa (National Social Register) — wanda ke wakiltar kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 70, gidaje miliyan 8.1 sun riga sun samu aƙalla sashe ɗaya na tallafin Naira 25,000.
Wasu daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin sun samu sau biyu zuwa uku, dangane da sakamakon tantancewar da aka gudanar.
Ya kuma ƙara da cewa gidaje miliyan 2.2 sun samu kuɗin a zagaye na baya-bayan nan, bayan da aka tabbatar da lambar BɓN da NIN ɗinsu.
Edun ya danganta jinkirin da aka samu da rashin cika shirin rijistar NIN, amma ya jaddada cewa duk wasu kuɗaɗen da suka rage za a kammala rabawa kafin ƙarshen shekarar 2025.
