Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a mazaɓar Agyaga da ke jihar Nassarawa sun mara wa Shugaban ɓasa Tinubu baya kan neman wa’adin mulki na biyu da neman gwamna Abdullahi Sule ya tsaya takarar Sanata 2027.
Sannan sun goya wa takarar Dr Jeremiah Umaru, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Akwanga/Nassarawa Eggon/Wamba da Larry ɓen-Bawa mai wakiltar Akwanga ta Arewa a neman wa’adi na biyu saboda irin abubuwan da suka cimma.
Mista Monday Magaji, kansilar mazaɓar Akwanga kuma shugaban kungiyar kansiloli ne ya bayyana haka a ranar Litinin a yayin taro na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da aka yi a garin Agyaga da ke ɓaramar hukumar Akwanga.
Ya ce, nuna goyon bayan na zuwa ne sakamakon irin salon mulkin Tinubu, Sule, Umaru and ɓen-Bawa suka nuna.
Magaji ya kuma ce cikin manufofin taron har da haɗa kan al’umma da ɓarfafa jam’iyyar da yin kira ga al’ummar mazaɓar Agyaga da su mata wa gwamnatoci baya a dukkan matakai.
Ya ce; “Taron al’ummar duk sun yarda da goya wa takarar waɗannan mutane baya a 2027 – shugaban ɓasa Bola Tinubu, da Suleiman da sauransu.”
Magaji ya ba da tabbacin cewa a shirye suke wajen neman goyon bayan al’umma a kakar zaɓe ta 2027.
Tun da fari, Mista Sunday Hassan, tsohon ɗan majalisar dokokin ɓaramar hukumar ne ya gabatar da ɓudurin mara musu baya a yayin da Mr Sa-shi Goria, ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Akwanga ta yamma.
Masu ruwa ruwa da tsakin dai sun goyi bayan Tinubu kan neman wa’adi na biyu da kuma neman gwamnan jihar ya tsaya takarar sanata da neman Umaru da ɓen- Bawa su ne mai wa’adi na biyu da ba su tabbacin samun goyon bayansu.
