Kun yi sa’a shugabanmu mai bin doka da oda ne – Wike ga Sowore da masu sukar Tinubu

Spread the love

Ministan Abuja Nyesom Wike, ya yi wa ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Omoyele Sowore, kaca-kaca bisa sukar Shugaba Bola Tinubu.

Wike ya bayyana cewa babban sa’a ne a gare shi kasancewar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana mutunta doka da oda.

“Kai sa’ar da kayi shine, kana da shugaban kasa da yake bin doka. Ka ci gaba da samun wannan sa’a.”

Wike ya kuma ce, Sowore ya kira shugaban kasar “Ɓarawo, Ɗan Ta’adda” amma har yanzu yana yawo ba tare da an ɗauki mataki a kansa ba.

Ministan ya kara da cewa, wannan shi ne shaida cewa gwamnatin Tinubu ba ta take haƙƙin ƴan ƙasa, domin a karkashin wasu shugabanni, irin wannan kalamai da Sowore da ire-irensa ke furtawa na iya jawo masa mummunan sakamako.

Omoyele Sowore, wanda ya shahara da fafutukar kare haƙƙin ɗan-adam da adawa da cin hanci da rashawa, ya daɗe yana sukar gwamnati musamman ta Bola Tinubu.

By Babaji