ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya taya Maryamu Idris murnar nada ta a matsayin Wakiliyar Najeriya a OPEC.
Wannan bayanin na ƙunshe ne a wata takardar sanarwa ɗauke da sa hannun babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar Muhammad kaula ya fitar.
Maryamu, ‘yar asalin Jihar Katsina ce, kuma ita ce daraktar janar na NNPC Trading Limited.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana wannan muƙami a matsayin shaida ta ingancin ƙwararrun da Katsina ke samarwa domin hidima ga ƙasa da ma duniya baki ɗaya.
“Muna alfahari da ganin ‘yar Katsina ta samu damar wakiltar Najeriya a irin wannan babbar ƙungiya ta duniya,” in ji Dikko Raɗɗa.
Ya bayyana ƙwarin gwiwa cewa Maryamu za ta yi amfani da gogewarta a fannin man fetur wajen kare da kuma inganta muradun Najeriya a ƙungiyar OPEC.
Gwamnan ya kuma nuna cewa wannan muƙami na daga cikin shaida ga manufar shugaban ƙasa Bola Tinubu na baiwa ƙwararru ko ina cikin Nijeriya manyan muƙamai ba tare da la’akari da ko wace jiha ba.
Gwamnan Raɗɗa ya yi wa Maryam fatan nasara kan aikin ta da jan hankalin ta da ta cigaba da zama jakadiyar kirki ga jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya.
