Fiye da rabin ƙananan yaran Afirka na rayuwa cikin ƙangin talauci – Rahoto

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wani sabon rahoton bankin duniya da asusun tallafa wa ƙananan yara na Unicef ya nuna cewa a yankin Afirka, kudu da hamadar sahar ƙangin talauci tsakanin ƙananan na ci gaba da ƙaruwa.

Rahoton ya ce fiye da rabin ƙananan yaran Afirka na rayuwa cikin ƙangin talauci, inda ya ce yaro guda cikin kowane biyar na rayuwa cikin ƙangin talauci a duniya.

To sai dai rahoton – wanda aka fitar a cikin wannan wata na Satumba – ya nuna cewa adadin yaran da ke rayuwa cikin ƙangin talauci ya ragu daga miliyan 507 zuwa 412 tsakanin 2014 zuwa 2024, yayin da Indiya ke kan gaba a samun ci gaban.

Rahoton ya ce ƙasashen Kudancin Asiya sun samu nasarar rage yawan yaran da ke rayuwa cikin ƙangin talaucin da kusan fiye da rabi.

”ƙasashen Afirka, kudu da hadamar Sahara ne ya ƙunshi kusan kashi 23 na ƙananan yara a duniya, kuma yankin ne ya ƙunshi kashi uku cikin huɗu – fiye da miliyan 312 – na yawan duka yaran da ke fama da ƙangin talauci a duniya,” kamar yadda rahoton ya nuna.

Rahoton ya nuna cewa tun 2014 kashi 52 cikin 100 na yaran yankin na rayuwa cikin ƙangin talauci.

Sabon rahoton ya ƙayyade cewa duk gidan da ke rayuwa a ƙasa da dala uku, yaran gidan na rayuwa cikin ƙangin talauci.

By ukarofi