Daga MUAZU HRɗAWA a Bauchi
Hukumar Samar da Ayyukan Yi ta ƙasa (National Directorate of Employment (NDE) za ta horas da mutane dubu 41 a Nijeriya, yadda mutane 1032 suka samu shiga cikin shirin daga jihar Bauchi, domin amfana daga nau’in sana’o’i sama 30 da za su taimakawa mutane wajen samun dogaro da kai.
Cikin jawabinsa Kodinetan hukumar ta NDE a jihar Bauchi Alhaji Ilya Yakubu Ilela wanda ya karanta jawabin shugaban hukumar na ƙasa Mr. Silas Ali Agara, ya bayyana cewa shirin an fara ƙaddamar da shi a matakin ƙasa ranar 6 ga watan Disamba, 2024 a karon farko don cika ƙudirin gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu don ƙarfafa tattalin arzikin mutane da magance talauci a ƙarƙashin ma’aikatar ƙwadago ta tarayya.
Ya ƙara da cewa a lokacin shirin na farko an horas da mutane dubu 32,692 a jihohi 36 da Abuja, don suma idan sun koya su horas da matasa sana’a daban-daban da kowa zai iya dogaro da kansa.
Daga bisani mutane 5532 sun samu cin moriyar samun rancen kuɗin da ya taimaka musu wajen tsayawa da kafafunsu a fannin ci gaba da neman abin kan su.
Cikin shirin samun horon na NDE a karo na biyu wanda aka ƙaddamar ranar Alhamis 4 ga Satumba, 2025 a Bauchi, an fara horas da mutane dubu 41,307 a matakin ƙasa.
Haka kuma za a koyar da Sana’a sama da nau’i 30 wanda suka kunshi samun horo a fannin aikin gona da sarrafa fasahar zamani ta ICT da sauransu.
Shugaban hukumar ta NDE a ƙasa Silas Ali Agara ya ƙara da cewa daga shirin farko da aka ƙaddamar sun samu ci gaba ta hanyar neman shiga ta hanyar yanar gizo, yadda aka buɗe zauren yanar sadarwar zamani don tabbatar da adalci wajen ɗaukar masu cin gajiyar shirin.
Kuma an ɗauki mutane huɗu a kowace mazaɓar jefa ƙuri’a 8809 a ake da su a Nijeriya.
Don haka cikin mutane dubu 411 da suka nemi shiga cikin shirin, an ɗauki mutane dubu 41,307 kuma tuni sun ci gaba da samun horo.
Haka kuma bayan sun kammala samun horo za a ɗauki mutane dubu 14,457 don ba su rancen kuɗin da zai taimaka musu tsayawa da ƙafafun su don ci gaba da neman abin kan su har suma su taimaka wajen horas da wasu.
Hajiya Zainab Baban Takko kwamishinar mata ta jihar Bauchi ita ce ta wakilci Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir na jihar Bauchi da uwargidansa Hajiya Aisha Bala Mohammed a wajen taron, yadda ta yaba da wannan shirin kuma ta bukaci wanda suka samu shiga kan su mayar da hankali wajen lura da abin da ake koya musu. Haka kuma gwamnatin jihar Bauchi zata duba yiwuwar taimakawa don ganin an fadada yadda za a sake daukar wasu mutane don horas da su.
Injiniya Salmanu Mohammed tsohon Darakta a hukumar ta NDE cikin jawabinsa ya bayyana cewa an ƙirƙiro hukumar tun zamanin mulkin Soja a karkashin doka ta 24 a shekarar 1989 da nufin ganin kowane dan kasa ya samu abin yi ta hanyar dogaro da kai. Ya ce a matsayinsa na injiniya wanda ya jima da yin ritaya kuma ya tsufa, amma har yau yana gyaran motoci don ci gaba da samun arzikin da zai riƙe kansa da iyalansa.
Kasimu Shehu Gamawa shine ya wakilci ma’aikatar kwadago ta tarayya a wajen taron, Shima ya ja hankalin matasan da su sani kowa daga cikin su mai samar da aiki ne ga mutane saboda gwamnati baza ta iya ba kowa aikin yi ba, don haka ya kamata kowa ya mai da hankali ya koyi sana’a don ya riƙe kansa ya taimaki wasu masu tasowa.
Mutane da dama sun yi jawabi, cikin su akwai Alhaji Usman Ilela daga hukumar SMEDAN da Alhaji Garba Jibrin Kirfi da Hajiya Zainab Mohammed da kuma shugaban hukumar lura da shiyyar arewa maso gabas NEDC na jihar Bauchi Alhaji Aliyu Ishak da sauran manyan baƙi.
Cikin jawaban su akasari sun buƙaci kowa ya himmatu wajen koyon abin da ya kawo shi wannan waje don ya amfana shi ma wani ya amfana daga gare shi.
An ɗauki ɗaliban daga tsakanin shekara 18 zuwa 40 kuma kowa zai riƙa samun Naira dubu biyar a kowane wata cikin asusun ajiyarsa na don rage kuɗin abin hawa har na tsawon watanni uku da za su ɗauka ana ba su horon.
