Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya nesanta kansa daga wata magana mai cike da cece-kuce da wani Kola Johnson ya yi iƙirarin cewa shi ne mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai.
Sanarwar wadda ta yaɗu a ranar Larabar da ta gabata, ta yi zargin cewa Atiku ya yi alƙawarin bai wa Yarabawa fifiko idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027.
Haka kuma ya nuna cewa gwamnatin Atiku ba za ta fifita wata ƙabila fiye da wata ba, saboda alaƙar aurensa da yankin Kudu maso Yamma.
Sai dai a wata kakkausar murya da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe ya fitar a ranar Alhamis, Atiku ya bayyana iƙirarin a matsayin “ƙarya, cin zarafi, da kuma farfaganda da gangan da nufin raina shi a kafafen yaɗa labarai.”
Atiku ya dage cewa bai taɓa saka Kola Johnson a matsayin mataimaki, mai ba da shawara ko abokin tarayya ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “A bayyana a sarari: Atiku Abubakar bai taɓa ɗaukar Kola Johnson a matsayin mai ba da shawara, ko mataimaki ko abokin tarayya ba.
Jigon na PDP ya zargi Fadar Shugaban ƙasa da ɗaukar nauyin ‘yan amshin shata da ‘yan jaridun ƙarya a wani yunƙuri na ɓata sunan shugabannin ‘yan adawa.
“Binciken da muka samu yana nuni ne kai-tsaye ga fadar shugaban ƙasa, wadda a cikin matsayar ta na ɓata wa shugabannin ‘yan adawa suna, ta ɗauki hayar marasa aikin yi don ƙirƙirar labaran ƙarya da kuma yaɗa maganganun da ba su da tushe ga Atiku,” inji Ibe.
Ofishin yaɗa labarai na Atiku ya buƙaci ‘yan jarida, editoci, da gidajen yaɗa labarai da su yi taka-tsan-tsan tare da tabbatar da sahihancin duk wata magana da aka dangana masa kafin a buga.
“An shawarci Editoci da kafofin watsa labarai da su tabbatar da ofishin watsa labarai na Atiku kafin a buga labari,” inji sanarwar.
Ya kuma ƙara da cewa, mai baiwa Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai ko kuma mataimaki na musamman kan harkokin sadarwar jama’a ne kaɗai ke da ikon fitar da bayanai a hukumance a madadin sa.
Rahoton mai cike da cece-kuce ya ruwaito Johnson yana iƙirarin cewa Atiku ya tabbatarwa masu ruwa da tsaki a Kudu maso Yamma kan ƙudurinsa na cimma muradun Yarrbawa, yana mai nuni da cewa ya daɗe yana da alaƙa ta aure da al’adu da yankin.
