Harin masallaci: An gudanar da jana’izar mutum biyar da ‘yan ta’adda suka kashe a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

An gudanar da jana’izar mutum biyar da ‘yan ta’adda suka kashe a yayin da suke gudanar da sallar Asubahi a garin Yandoto da ke ƙaramar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara yanzun nan. Sallar jana’izar ta samu halartar ɗaruruwan al’ummar musulmi daga lungu da saƙon ƙaramar hukumar ta Tsafe

Idan ba a manta ba, wasu gungun ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a lokacin da ake tsaka da sallar Asuba a garin Yan Doto da ke ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

‘Yan ta’addar sun kashe mutane biyar tare da yin garkuwa da wasu da dama a halin yanzu.

Wani mazaunin garin mai suna Malam Jamilu Yandoto, ya shaida wa Wakilinmu ta wayar tarho cewa, ‘yan bindigar sun yi wa masallacin ƙawanya da misalin karfe 5:30 na safiyar yau inda suka kulle masallacin tare da fara harbe-harbe a lokacin da masallatan ke gudanar da sallar Asuba.

A cewarsa, an yi garkuwa da wasu masallatan da dama, inda ya ƙara da cewa wasu kuma sun samu munanan raunuka a harbin da ƴan ta’addan su kayi masu a yayin harin.

“Kamar yadda nake magana da kai, yanzu haka mun rasa mutane biyar kuma muna shirin kai waɗanda suka samu raunuka zuwa Gusau domin yi musu magani”. Yace

Garin Yandoto shine mahaifar fitaccen ɗan siyasan nan a Jihar Zamfara, Sanata Kabiru Garba Marafa, mai tazarar kilomita 31.6 daga Gusau babban birnin Zamfara.

Hakazalika, duk ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar ya ci tura daga wakilin mu a lokacin haɗa wannan rahoton.

By ukarofi