Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Fursunoni 68 da ke tsare a gidan yarin a jihar Kano ne suka samu sakamako mai kyau a jarrabawar NECO ta bana.
Waɗannan fursunoni da suka samu nasarar sun samu kiredit 5 zuwa sama ciki har da Lissafi da Turanci. Waɗannan dai na cikin dubban mutanen da suka samu tallafin karatu ne daga gwamnatin Kano.
Wannan dama ta yin karatu na cikin dokar kula da gidajen yari ta shekarar 2019 wanda ya ƙunshi gyaran hali da sauya halin fursunonin ta hanyar ilimantar da su da ba su horo.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya biya sama da Naira biliyan 3 a watan Maris ga ɗalibai 141,175 da suka haɗa da har da fursunoni da suka rubuta jarrabawar NECO, NABTEB a Kano.
Wannan kuɗi na cikin biliyoyin kuɗin da gwamnatin ta zuba hannun jari a ɓangaren ilimi baya ga kaso 26% na kasafin kuɗin da aka ware wa ɓangaren ilimi.
A cikin jawabin da mai magana da yawun hukumar kula da gidajen yari ta Kano, Musbahu Lawan ƙofar Nassarawa, ya ce, fursunonin sun yi nasara ne bayan tsage damtse wajen karatu.
Shugaban gyaran hali na Kano, Ado Inuwa, ya nuna jin daɗinsa kan yadda fursunonin suka yi ƙoƙari tare da yi musu fatan samun nasara wajen inganta rayuwarsu.
Shugaban ƙungiyar nemawa fursunoni rangwame, Azumi Namadi Bebeji, an rawaito ta tana taya fursunonin murna kan nasarar da suka samu tare da yaba wa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf kan tallafa musu da ya yi.
A kwanakin baya ne hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta ƙasa (NECO) ta saki sakamakon jarrabawar ɗaliban da suka rubuta jarrabawar a bana, inda jihar Kano ta zo ta ɗaya a Nijeriya wajen yawan ɗaliban da suka samu kiredit sama da 5 ciki har da Lissafi da Turanci.
