Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya ƙaryata zargin cewa ya taɓa neman wa’adi na uku a lokacin mulkinsa.
Ya bayyana hakan ne a taron tattaunawar dimokraɗiyya da aka shirya a Accra, Ghana ta gidauniyar Goodluck Jonathan.
Obasanjo ya ce babu wani ɗan Nijeriya, raye ko mamaci, da zai iya gaskata cewa ya taɓa roƙon goyon bayansa don samun wa’adi na uku.
Ya ce: “Ni ba wawa ba ne, idan ina son wa’adi na uku, zan san yadda zan yi. Kuma babu wanda zai ce na taɓa kiran sa na ce ina son na yi wa’adi na uku.”
Ya kuma ƙara da cewa samun yafiya ga bashin da Nijeriya ta ciyo a lokacin nasa mulki ya fi wahala fiye da neman wa’adi na uku, amma ya cimma hakan.
Ya gargaɗi shugabanni da ke yin dogon zama kan mulki, yana mai cewa tunanin cewa babu wani da zai iya maye gurbinsu babban zunubi ne ga Allah.
Obasanjo ya jaddada cewa shugabanci ya kamata ya kasance hidima ce, ba matsayin da za a riƙe da dole ba.
A nasa jawabin, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ce shugaban da ya gaza ya kamata a cire shi ta hanyar ingantaccen zaɓe.
Ya yi gargaɗin cewa maguɗin zaɓe na daga cikin manyan barazana ga dimokuraɗiyya a nahiyar Afrika, yana mai cewa idan ba a sake tunani da gyara tsarin ba, dimokuraɗiyyar na iya durƙushewa.
Jonathan ya ce ’yan Afrika na buƙatar dimokuraɗiyya da ke tabbatar da ’yancinsu da sahihin zaɓe da tsaro da ilimi da aiki da lafiya da mutunci.
