Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
ɗaya daga cikin dattawan babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ya ce za su ci gaba da yin gwagwarmaya da ƙoƙarin haɗakan duk wani mai faɗa-aji a siyasar Nijeriya don tabbatar da ci gaban ƙasar da ma dimukraɗiyya.
Alhaji Sule Lamido, wanda tsohon gwamnan jihar Jigawa ne, ya shaida wa BBC cewa ya sha faɗin cewa idan kana tunkarar abu, to baka kawo rashin nasara a cikinsa.
Ya ce,”Ko shakka babu muna ta faɗi tashin ganin mun yi sulhu a inda ya kamata a yi, sannan muna wayoyi da tuntuɓa domin Nijeriya ta ci gaba, kuma mu abin da muke yi ba don kanmu muke ba don al’ummar ƙasar muke yi.”
Tsohon gwamnan na Jigawa, ya ce,” Mu dai wannan aikin da muke na haɗakan duk wani mai faɗa-aji a siyasar Nijeriya don ci gaban ƙasarmu, muna fatan Allah ya ba mu nasara.”
Ya ce,” A cikin abin da muke ba ma hangen cewa kada a nan gaba mu zo mu kasa ko don saboda wani yana shugaban Nijeriya, mu zamu zamu ci gaba babu abin da za a faɗa don ba zamu kwanta muna ganin abubuwa na lalacewa a ƙasarmu ba.”
Alhaji Sule Lamido, ya kuma ce a cikin abubuwan da ya ke har da ƙoƙarin da suke yi wajen warware rikicin jam’iyyarsu ta PDP.
A baya-bayan nan Alhaji Sule Lamido, ya gana da wasu manyan ‘yan siyasa a Nijeriya, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar.
Alhaji Sule Lamido, ya ce,” Ni da mun yi PDP, a lokacinsa mun ci zaɓe inda ya zama mataimakin shugaban ƙasa, ni kuma ina ministan harkokin wajen, don haka yanzu muna zumunci sosai.”
Ya ce,” Ba Atiku kadai ba wanda yanzu bama jam’iyya ɗaya, ni ina haɗuwa mu tattaunawa da mutane da dama waɗanda ada mun yi jam’iyya daya yanzu kuma mun raba gari, dukkanmu ‘yan Nijeriya ne muna kuma so kasarmu ta ci gaba don haka don na hadu da wani ɗan jam’iyya mun tattauna ai ba laifi ba ne.”
“Shugaba Tinubu ba mun haɗu da shi a kwanakin baya mun kuma gaisa saboda a baya mun yi jam’iyya ɗaya wato SDP, kuma yanzu shugaban na ne saboda shugaban kasata ne, don haka ko ina so ko bana so ina da haƙƙi akansa, kuma idan na ga ya yi ba daidai ba zan faɗa masa ai gyara ne ba wai suka ba,” inji shi.
Tsohon gwamnan na Jigawa, ya ce,” Ba ni ba, duk wani dan Nijeriya yana da hakki akan shugaba Tinubu, kuma idan an ga yana bai daidai b aba laifi ba ne a faɗa gaskiya tun da gyara kayanka baya zama sauke mu raba.”
