Za mu ɗauki mataki kan Malam Lawan Triumph bayan samun ƙorafi a rubuce – Gwamnan Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa, da zarar gwamnatinsa ta amshi ƙorafi a rubuce kan malamin addinin Musulunci, Sheikh Lawan Abubakar, wanda ake kira da Triumph, za ta ɗauki matakin da ya dace akan sa.

Wasu mazauna birnin Kano sun yi zanga-zangar lumana game da zargin malamin addinin, Lawan Triumph da kausasa kalamai kan Annabi Muhammadu (SAW).

Masu zanga-zangar sun dangana da farfajiyar gidan gwamnatin Kano, inda Gwamna Abba ya tarɓe su tare da yi musu jawabi.

A baya-bayan nan ne aka ga malamin a wani bidiyo yana musanta batun cewa, haihuwar Annabi da kaciya ko kwalli, kamar yadda wasu litattafai suka ruwaito, ba karama ba ce, saboda “ana iya haihuwar sauran mutane ma da kaciyar”.

A cewar malamin, karama na nufin “wani abin al’ajabi da Allah yake bai wa annabawa su kaɗai”. Kazalika, malamin ya ce, ruwayoyin ba su inganta ba, domin hatta tunkiya ma ana iya haihuwar ta da kwalli a idonta.

Gwamna Abba ya umarci masu ƙorafin su kwantar da hankali, inda ya nemi su rubuto masa takardar koke a hukumance ta hannun ofishin sakataren gwamnati.

“In Allah ya yarda za mu ɗauki matakin da bai saba wa Shari’a ba,” inji gwamnan.

“Abin da nake so shi ne ku koma ku rubuto wa gwamna takarda, wadda ita ce za a yi amfani da ita daga nan har zuwa kotun ƙoli.”

Masu ƙorafin sun amince su kai wa gwamnan takardar da ya nema da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar Alhamis. 

By ukarofi