Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Dan Majalisar Wakilai Yusuf Gagdi (APC a Filato) ya yi watsi da yunƙurin samar da ’yan sandan jihohi a Nijeriya.
Gagdi, mai wakiltar mazaɓar Pankshin/Kanke/Kanam, ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da ya ziyarci al’ummomin da ke fama da rikici a ƙaramar hukumar Kanam ta jihar Filato.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya bayar da rahoton ƙaruwar ‘yan bindiga a garuruwan Garga, Kukawa, Kyaram, Gyambau, Dungur da Shuwaka na yankin ƙaramar hukumar.
Satar mutane don neman kuɗin fansa da sauran nau’ikan laifuka na zama lamari mai tada hankali a cikin wazannan al’ummomin da abin ya shafa, wanda ke ƙara fargaba a tsakanin mazauna yankin.
Gagdi, a maimakon haka, ya ba da shawarar ƙarin kuɗaɗe ga hukumomin tsaro, yana mai jaddada cewa ‘yan sandan jihohi ba za su warware matsalolin tsaro da ke addabar Nijeriya ba.
Ya ƙara da cewa, mai yiwuwa gwamnonin za su yi amfani da ‘yan sandan jihar ba tare da ɓata lokaci ba, inda za su yi amfani da su wajen yaƙi da abokan gaba na siyasa maimakon samar da tsaro na gaskiya da zaman lafiya.
“A matsaya ta, ko da a zauren majalisa, gwamnonin za su yi amfani da ‘yan sandan jihohi, musamman a kan ‘yan adawar siyasa, ba don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba.
“Na faɗi haka ne ba tare da fargabar samun saɓani ko bata-kashi a siyasance ba, Nijeriya ba ta isa ta yawaitar hukumomin tsaro ba.
“A maimakon haka, ina goyon bayan ƙarfafa hukumomin tsaro da ake da su, a ba wa ‘yan sanda, soji, ma’aikatar harkokin gwamnati da sauran su kuɗaɗen da suka dace, da kuma tabbatar da alhaki,” inji Gagdi.
Ya tsaya tsayin daka na kin yin kwafi ko ruɓanya hukumomin tsaro da sunan baiwa wasu mutane ikon ‘yan sandan jiha.
Gagdi ya buƙaci gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su gudanar da aikin share fage a dazuzzukan da ke kan iyakokin Filato, Taraba da Bauchi domin fatattakar masu aikata laifuka.
ɗan majalisar ya ce ziyarar ta ba shi damar tantance halin da ake ciki na tsaro a yankunan da lamarin ya shafa.
Ya kuma gargaɗi jami’an tsaro kan yin sulhu, ya kuma shawarci mazauna yankin da su kare kansu bisa ƙa’ida, cikin iyakokin da doka ta tanada.
