Mawallafin jaridar PRNigeria ya maka makarantar NIPSS a kotu kan cire shi daga kwas na 47

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wanda ya kafa PRNigeria, Malam Yushau A. Shuaib, ya shigar da ƙara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda yake ƙalubalantar cire shi daga kwas ɗin SEC 47 na Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru ta ƙasa (NIPSS) ta Kuru da ke Jihar Filato.

A cikin ƙarar mai lamba THC/ABJ/CS/1329/2025, shahararren masani kan hulɗa da jama’a, Shu’aib, yana buƙatar a biya shi diyyar Naira Biliyan 1, da kuma ƙarin diyya a kan NIPSS bisa zargin tada masa hankali da kuma ci masa mutunci. Har ila yau, yana neman ƙarin Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin ƙara, bayan da ya bayar da sanarwar ɗaukar matakin a ranar 16 ga watan Yuni, 2025, ga Babban Darakta na Cibiyar, Farfesa Ayo Omotayo, wanda hukumar ta yi watsi da ita.

Shari’ar da wani Babban Lauya a Nijeriya (SAN) Yunus Abdulsalam ya shigar a madadinsa, yana neman kotu ta bi masa haƙƙin sa kan cire shi daga SEC 47 da kuma mayar da shi bakin aiki da cikakken haƙƙi da walwala. Shuaib yana kuma neman wata doka ta har abada da za ta hana NIPSS da jami’anta ci gaba da cin zarafinsa ko tsoratarwa.

A farkon sammacin da ya gabatar, wanda ya shigar da ƙarar ya gabatar da batutuwa takwas don tantancewa. Ya ƙara da cewa, buga labarin da wata ƙungiya mai zaman kanta ta PRNigeria ta wallafa, wata ƙungiyar yaɗa labarai mai zaman kanta ba za a iya danganta shi da rashin ɗa’a ba. Ya kuma yi tambaya kan ko tuhumar da NIPSS ta yi na shiga da yin amfani da imel na sirri ba tare da izini ba ya keta haƙƙinsa na sirri na tsarin mulki a ƙarƙashin sashe na 37 na kundin tsarin mulkin 1999.

Shu’aib ya kuma ƙara da cewa, matakin ladabtarwa da aka yi masa kan ra’ayoyin kwararru da ya bayyana a cikin wata makala da aka buga ya keta haƙƙinsa na faɗin albarkacin baki da sashi na 39(1) ya lamunce. Ya bayar da hujjar cewa hana mahalarta mu’amala da shi da kuma cire shi daga dandamali na hukuma ya kasance cin zarafi ta yanar gizo, da tilasta warewa.

Ya ci gaba da cewa hana shi shiga rangaɗin karatu na ƙasa da ƙasa, duk da cikakken biyansa kuɗaɗen kwas da ya kai Naira miliyan 18.3, ya zama nuna wariya da karya kwangila. Ya kuma nuna rashin amincewa da dakatarwarsa da janyewarsa daga kwas ɗin bisa zargin “bare batun” ba tare da sauraron shari’a ba, yana mai bayyana hakan a matsayin take haƙƙinsa na tsarin mulki ƙarƙashin sashe na 36(1).

Don haka Shuaib yana neman bayyana cewa ayyukan NIPSS sun saɓa wa doka, rashin gaskiya, nuna wariya, da rashin goyon bayan kowace doka da ke jagorantar cibiyar.

By ukarofi