
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya yi watsi da rahotannin da ke cewa yana da niyyar janyewa daga tsayawa takara domin bai wa wani ɗan takarar shugaban ƙasa damar tsayawa a zaɓen 2027.
Atiku, a wata takarda da mai ba shi shawara kan harkar yaɗa labarai, Paul Ibe ya fitar, ya bayyana ikirarin a matsayin kuskure game da wata hirar da BBC Hausa ta yi da shi.
Ibe ya ce, nazari mai zurfi da aka yi akan hirar ya nuna cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar bai faɗi haka ba ko nuna yana da shirin janyewa.
A cewarsa, abinda mai gidan nasa ya ce shi ne “matasa da sauran masu muradin tsayawa takara, suna da damar shiga a gwabza da su.”
Ya kuma ce, idan wani matashin ɗan takara ya yi nasara a zaɓen fidda gwani, to zai goya masa baya ba tare da la’akari da wani abu ba.
Don haka, ya yi watsi da batun janyewar da wasu kafafen labarai suka yaɗa, yana mai cewa ba haka yake nufi ba.
Da fari, an ruwaito cewa Atiku a wata hira da BBC Hausa ya ce zai janye daga batun tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 muddin wani matashin ɗan takara ya doke shi a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar ADC.
