Jami’ar ABU sadaka mai wanzuwa ga gamji!

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Bayan bawa ya koma ga Allah bias koyarwar addinin Islama da Firimiya Sir Ahmadu Bello ya koma ga Allah a kai, duk ayyukan sa na lada sun yanke sai sadaka mai wanzuwa da su ka hada da kafa wani abu na alheri da mutane su ke cin moriyarsa. Aƙalla a ce ka dasa bishiya ko ka tona rijiya da bayan baka nan mutane su ke cin moriya to za ka cigaba da samun lada. Firimiya ya jagoranci shuka alheri a lokacin rayuwar sa ya jajirce wajen kafa jami’ar ABU a Zaria da manufar al’ummar da za su zo a baya su shiga don samun ilimin addini da na zamani a tsarin zamani. Ba mamaki wani ya ce ai da kudin gwamnati ne ko ta amfani da gwamnati a ka assasa katafariyar jami’ar. Shin a nan in wata cibiya ta sharri a ka kafa fa inda a ke caca, zunduma rawa da shan kamru uwar laifi a ka yi amfani da dukiyar ta gwamnati? Don haka in an ba ka dama ta jagoranci ka tabbatar da adalci da ya ci gaba da wanzuwa bayan rayuwar ka za ka ci gaba da kwasar lada hakanan in sharri ka shuka ya wanzu bayan rayuwar ka. Idan ka ziyarci jami’ar Ahmadu Bello a Zaria ka ga yanayin girman ta a nan Samaru, Kongo da ma a Funtua zuciyar ka ka iya cusa ma ka yin addu’ar alheri ga wanda ya jagoranci kafa wannan waje mai muhimmanci ga dukkan al’ummar Arewa, Nijeriya da ma dukkan duniya. Zai yiwu wani ya ce ai cibiyar boko ce ba addini ba. Nan ma rashin fahimta ne don in ka yi karatun boko ta injiniya, likita, aikin nomad a sauran su ka fito ka ba wa al’umma gudunmawa da abun da ka koya ka yi abun da addinin ya ke so. A gefe guda ma akwai tsangayar Islama a jami’ar da za ka samu duk fannonin ilimi da ka ke buƙata don yi wa addinin hidima. Niyyar alheri da adalci ga kowa wajen kafa irin wannan cibiya ta zama abun farin ciki da yi wa jagora fatan rahama daga Allah. Ba ma musulmi ba, kowa jami’a za ta yi ma sa amfani don manufar ita ce ya yada ilimi. Shin harshen Turanci ka ke son koya ko Larabci ko gwanancewa a harshen Hausa duk za ka samu biyan bukata daga nan jami’ar ABU a Zaria zuwa kan ‘yar uwar ta jami’ar Bayero da ke Kano. Abun nema ga jagora ya shuka alheri don jama’a ba don kashin kai, iyali ko dangi ba. Amadu Sadauna ya yi wannan aiki don burin sa na bunkasa ilimi a Lardin Arewa kuma ya cimma nasara a lokacin da Allah ya ara ma sa ya jagoranci Lardin kakaf. Abun nema gwamnoni na Arewa su yi koyi da irin jagorancin Sardauna wajen shuka alheri a jihohin su don amfanin dukkan al’umma ba riya ba.

Marigayi Firimiya Sir Ahmadu Bello tamkar mikiya ce mai hangen nesa. Ba ma sai an yi wasu misalai masu yawa ba, in an duba yanda ya shimfiɗa taswirar gina katafariyar jami’ar Arewa ABU Zaria ta kwanta ta nufi Funtua za a gane aiyukan sa ma akasari don jama’ar da ke zuwa a baya ne su ci gajiya. A lokacin an yi mamakin girman filin da a ka dauka don gina jami’ar, amma yau duk wanda ya shiga Zaria ya ga yadda a ka yi gine-gine na tsangayoyi daban-daban a wadace zai gane abun da Gamji ya hango. Ko a lokacin da a ka buɗe jami’ar a 1962 da ɗalibai 426 guda 147 kacal  ne ‘yan Arewa da hakan bai karya guiwar Sardauna wajen hango bunƙasar da jami’ar za ta yi bayan rayuwar sa ba. Don rashin ‘yan bokon da matsayin su ya kai zama mataimaka shugaban jami’a “ɓice chancellor” Bature ne dan ƙasar New Zealand Dr. Norman S. Aleɗander ya jagoranci jami’ar zuwa lokacin ajiye aikin sa a 1966 ya samu nasarar kara gine-gine da ɗaukar ɗalibai da yawan su ya kai kimanin 1000. Wani abun farin ciki ga yanda Allah ya taimaki Gamji shi ne bayan kammala jagorancin Dokta Aleɗander da ma yin kisan gilla ga Gamjin, sai a ka nada mukarrabin sa kuma likitan sa Farfesa Ishaya Audu ya zama ɗan ƙasa na farko da ya riƙe mataimakin shugaban jami’ar ABU har zuwa 1975. Farfesa Ishaya Audu wanda a ka haifa a Anchau ta Zazzau, Bahaushe ne mabiyin addinin kirista har ya koma ga Allah a 2005. Mahaifin Farfesa Ishaya wato Mr.Bulus na daga Hausawa na farko da su ka bar Musulunci su ka shiga addinin Kirista a karni na 20 don fahimtar su nan ne hanyar gaskiya.

Idan a na ba ku sahihan labarun alaƙar alheri da ta wanzu tsakanin Farfesa Ishaya Audu da Gamji Ahmadu za ku zubar da hawaye don ganin halin rashin zumunci da ya keta al’ummar Arewa na yau. Farfesa Audu ne likitan Arewa na farko da ya zama farfesa. Irin ɗabi’un Sir Ahmadu Bello na mutunta kowa ba ya nuna bambancin addini ko kabila sam. Duk mai bin addinin Kirista da ya yi aiki da Gamji kan samu tunatarwa cewa yau Lahadi ne shirya ka tafi majami’a ka yi ibadarka. Mun samu labari a ziyarar sa ƙasar Iran sai da ya buƙaci a sauke shi a anguwar da ke daf da majami’a don a ranar Lahadi Farfesa Audu ya samu wajen ibada.

Hatta ɗan ƙabilar Igbo Chukwuma Nzegwu Kaduna da ya dana kunamar bindiga ya harbe Sardauna, na daga cikin mutanen da kan shiga ko ina a gidan Firimiya don yadda Gamji ke ƙaunar jama’a. Dama an ce a wasu lokuta ka yi addu’ar kariya daga sharrin wanda ka taimaka. Babban direban Gamji wato Ali Sarkin mota ya ce a jajiberin juyin mulkin 15 ga Janairu 1966, Nzegwu ya ɗau ɗabi’ar bin Sardauna a baya duk inda ya shiga har kuma Gamji ya fahimci lallai akwai makircin da ya ke kullawa. Hatta ma tarbar Ladoke Akintola da Sardauna ya yi a filin jirgi, Nzegwu na biye da shi ya na dube dube da ƙulla makircin yin kisan gilla. Marigayi gwamnan jihar Kudu maso yamma Akintola ya shaidawa Sardauna fargabar abun da ya ke has ashen zai faru amma Sardauna ya ba shi haƙuri da su tsaya kar su gudu ko ina. Gaskiya a wajen Sardauna tun da ya na dauke da haƙƙin jagorancin al’umma, gara ya zauna a cikin su in ya so komai zai faru bai watsar da amanar da a ka ɗaura ma sa ba. Haka Gamji ya zauna ya zaɓi ya yi shahada kuma hakan a ka yi a ka harbe shi a nan gidan Arewa inda yanzu haka kabarin sa ya ke. Abun farin ciki shi ne haƙiƙa an kashe Amadu amma sam ba a kashe aiyukan sa na alheri ba. Dududu Sarduna kimanin shekaru 54 ya yi a duniya amma kai ka ce 100 ya yi in an duba nasarorin da ya cimma. Mu dai tsakanin mu da Sardauna sai addu’ar Allah ya yi ma sa rahama ya kuma dawo da annurin Arewa na zamanin Sardauna ko ma dan sarara daga fitintinun zamanin nan inda dan kankanin yaro da ba a dade da sauke shi daga zanin goyo ba, zai kalli al’ummar Arewa ya aibanta Sardauna kuma ya kwana lafiya. Allah ya ba mu lafiya ‘yan uwa.

KAMMALAWA

Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ita ce hamshakiyar cibiya abar alfahari ta Arewa da wasu cibiyoyin ilimi mai zurfi su ka biyo bayan ta. Hamshaƙan ‘yan boko na Arewa da dama sun yi karatu a wannan jami’a kuma su kan yi tinƙaho da cewa a nan su ka kammala makaranta. Wannan ya kai ni ga kira ga waɗanda su ka yi karatu a jami’ar da can da ke raye da ma matasa na yanzu su tashi tsaye wajen kare martabar Arewa. Illa iyaka. Gudunmawar da ɗaliban jami’ar ABU za su bayar da za ta yi matuƙar tasiri a wannan zamani da makirci ko annamimanci ya koma tunzura mutane da labarun karya don tada fitina ta yanar gizo ita ce ta fito da sahihan bayanai na tarihi don amfanin duk jama’ar da za ta zo nan gaba. Kazalika su ƙirƙiro wata manhaja da za ta riƙa goge karairayin da a ke yadawa na ɓatanci ga Firimiya Amadu. Bude dandali a yanar gizo ko wata kafar labaru mai suna GAMJI da taken mazan kwarai zai yi matukar amfani ta fuskar zantawa da masana tarihi da cibiyar kula da gidan Arewa ta ke da su don akalla wanzar da kishin ƙasa da iyayen Arewa su ka yi wajen sadaukar da rayuwarsu, su ka karɓo ‘yancin ƙasa daga Turawa sannan su ka ba da ran su gaba ɗaya don hidima ga ƙasa da hakan ya sa miyagu su ka yi amfani da kunamar bindiga su ka sheƙar da jinin su. Na ga wasu na ba da shawara da dawo da darasin tarihi a makarantun firamare da sakandare. Wannan ma na tabbata zai yiwu da taimakon iya ɗaliban da jami’ar ABU ta yaye. Ni kai na na yi ƙoƙarin karatu a ABU don ganin wannan martaba amma a ka samu akasi lokacin wata zanga-zanga yayin da Farfesa Daniel Saror ke kujerar muƙaddashin shugaban jami’ar. Allah ya sa mu dace.

By ukarofi