Ban ce Buhari ya haɗa hannu da Boko Haram ba, inji Jonathan

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Toshon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya musanta rahotannin da wasu gidajen jaridu ke yaɗawa cewa ya zargi marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da zama mai shiga tsakani Gwmanatin Tarayyan gw Boko Haram a yayin da ake tsaka da fuskantar ƙalubalen ta’addancinsu.

A wata takarda daga mai taimaka masa akan harkar yaɗa labarai, Ikechukwu Eze, Jonathan ya bayyana cewa kalamansa a taron ƙaddamar da littafin tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Lucky Irabo (mai ritaya) abinda wasu gidajen jarida suke yaɗawa.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce ya nufi yin tsokaci ne akan dabaru da salon da Boko Haram ke amfani da su wajen aiwatar da z zayyukanta bisa nasara ciki har da lissafo sunayen sanannun ƴan ƙasa a matsayin waɗanda suka shiga tsakani yayin tattaunawa da su don samun zaman lafiya.

Ya bayyana cewa, shi abinda ya yi a taron shi ne bada misalin yadda mayaƙan suke amfani da sunayen wasu manyan ƴan ƙasa da nufin ruɗar da al’umma.

A cewarsa, ya kira sunan Buhari ne don bada ba’asin yadda mayaƙan suke amfani da ƙarfin yaɗa al’amarin labaransu ba wai don ya ɗora masa laifi ko wani ɗan ƙasa ba.

By Babaji