
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano ta sanar da kama wani matashi da ake zargi da yin awon-gaba da Hakimin Garun Babba, Alhaji Abdulmumini Mudi Zakari a jihar.
A sanarwar da Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Asabar, jami’an sashin yaki da satar mutane sun cafke wanda ake zargi mai suna Usman Lawan Baba, wanda aka fi sani da “Yellow,” mai shekaru 27.
An kama shi ne a ranar 2 ga Oktoba, 2025, a Dakatsalle na Gundumar Zango Ranka a Ƙaramar Hukumar Bebeji da ke jihar.
Rundunar ta ce bincike na cigaba da gudana domin gano sauran abokan aikinsa da kuma ceto sauran waɗanda ake zargin sun shiga lamarin.
Kakakin ya kuma tabbatar da cewa da zarar an kammala bincike akansa, za a miƙa shi ga kotu domin ya fuskanci hukuncin doka.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Ibrahim Bakori ya yaba da ƙoƙarin jami’an yaƙi da ayyukan garkuwa da mutane da mazauna yankin bisa gudumawar bayanan sirri da suke taimakawa da su domin daƙile ayyukan ɓata-gari acikin al’umma.
