
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimamin mambobin Majalisar Wakilai guda 89 da ke ƙarƙashin inuwar marasa rinjaye suka ja layi akan ba su amince da buƙatar cire shugabansu, Hon. Kingsley Chinda a muƙamin ba.
A yammacin yau Litinin za a gudanar da zaman ƴan ɓangaren a Abuja wanda zai haɗa da jagororin jam’iyyun PDP, LP, NNPP da YPP domin tattauna muhimman al’amuransu.
Hakan na zuwa ne bayan da Hon. Chinda ya shigar da ƙorafin shirin tsige shi da jagorancin majalisar ta 10 ke yi, lamarin da ya sa ɓangaren nasa ya kira taron gaggawa da za a gudanar a Otal ɗin ‘The Envoy Hotel’.
Hon. Chinda ya shigar da ƙarar ne domin a dakatar da Kakakin Majalisar, akawunta da wasu daga ɓangaren marasa rinjaye daga shirinsu na tsige shi a muƙamin akan zargin sa da rashin tsare aikin jagoranci da aiki wa jam’iyya mai mulki ta APC gami da kusancinsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike.
A ranar 7 ga watan Oktoba za a koma baki aiki a majalisa bayan hutun watanni biyu da ƴaƴanta suka tafi.
