Wajibi ne a fifita ƙasa akan maslahar kai – Gargaɗin Shettima ga PENGASSAN kan rikici da Ɗangote

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bayyana goyon bayansa ga Aliko Ɗangote a rikicin Matatarsa da ƙungiyar manyan ma’aikatan fetur da gas ta ƙasa (PENGASSAN), yana mai kira da a ƙaurace wa hakan da fifita kishin ƙasa da ɗaukar matakin tattaunawa domin kawo ƙarshen rikicin.

Shettima ya faɗi haka ne yayin buɗe babban taron harkar tattali na 2025 da aka gudanar a Abuja, inda ya jaddada muhimmancin matatar, wadda ke fitar da gangar mai 650,000 a kullum, don haka wajibi ne a tallafa masa ta kowane hali.

Ya ce, matatar mai darajar Dala biliyan 20 kadara ce ta ƙasa da ke buƙatar taimako domin aiwatar da ayyukanta yadda ya dace.

“Aliko Ɗangote ba mutum ɗaya ba ne, shi ɗin cibiya ce, kuma ginshiƙi ne ga tattalin arziƙi Nijeriya. Sannan yadda mu ke mu’amalantar wannan bawan Allahn shi zai nuna yadda ƴan ƙasar waje za su kalle mu”, inji Shettima.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya cigaba da cewa, “idan ya zuba jarin Dala biliyan 10 a Microsoft, a Amazon, ko a Google, da darajar arziƙinsa zai iya kai Dala biliyan 70 zuwa 80 i zuwa yanzu.”

Ya ƙara da cewa, attajirin ya zaɓi ya zuba jarin ne a ƙasarsa domin amfanin ƙasar da al’ummarta ta yadda za a samun bunƙasar al’amuran ciyar da ƙasar gaba.

By Babaji